Connect with us

MANYAN LABARAI

‘Yar Shekaru 19 Ta Kwace Acaba Ta Hanyar Amfani Da Kwaya

Published

on

Hukumar ‘yan sandan jihar Katsina ta sanar da cafke wata budurwa ‘yar shekaru 19 mai suna Zinatu Abubakar, wacce ake zargi da amfani da kwaya don ta kwace ma wani dan acaba babur.

A takardar da jami’in hulda da jama’a na hukumar, Gambo Isa, ya sanya wa hannu, ya shaida wa manema labarai, cewa budurwar ‘yar dab ace, cikin ‘yan daban da suka yi kaurin suna wajen kwacen babur a jihar Katsina.

Isa ya ce: wacce ake zargin ta yi kokarin amfani da kwaya akan dan acaban mai suna Gide Wada, ne a lokacin da ya dauke ta daga Kofar-Kaura zuwa rukunin gidaje na Sokoto Rima duk a cikin jihar Katsina.

‘Wada ya dakata a gefen hanya a lokacin da ya fara jin barci, bayan budurwar ta bashi alewar cakolet lokacin da ya dauketa a babur.’ Inji Gambo Isa
Advertisement

labarai