Mahdi M Muhammad" />

’Yar Shekaru 80 Ta Shiga Ajin Firamare Da Niyyar Zama Malama

Firamare

Wata tsohuwa ‘yar shekara 80 ta yi karatun firamare a wata makaranta da ke kauyen Bugandalo na cikin karamar hukumar Ibulanku ta kasar Yuganda, da nufin zama malami.

Maria Obonyo, wata manomiya, ta ce, bayan ta jimre wa wahala da zolaya, sai ta yanke shawarar zuwa makaranta don koyon yadda ake magana da rubutu da Turanci.

“Na yanke shawarar shiga makarantar ne saboda na rasa dukkan dangi na kuma babu wanda zai kula da ni. Na kukuri niyyar yin karatu har sai na kammala jami’ar Makerere a matsayin malama,” kamar yadda ta fada wa manema labarai.

A lokacin da Obonyo za ta kammala karatun makarantar ta, za ta kasance shekaru 96 a wannan lokacin. Tsohuwar, duk da haka, ta ce, a yanzu haka tana fuskantar tarin matsaloli, musamman rashin iya biyan kudin makaranta.

Babban malamin makarantar, Olibia Kwagala, ya ce, Obonyo ta sanya su alfahari da yin karatu a irin wannan shekarun kuma tana da yakinin za ta kammala ajin firamare na bakwai.

Kwagala ya kara da cewa, “Ta na kuma da matukar sha’awar koyon yadda za ta sanya hannu a kan wata takarda.”

Exit mobile version