A kokarinta na kawar da yaduwar cutar zazzabin cizon sauro musamman ga yara kanana da mata masu ciki, Gwamnatin jihar Kano zata raba magani ga yara kusan miliyan uku.Kwamishinan lafiya na jihar Kano.Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa ya bayyana hakan a hira da manema labarai dan kaddamarda makon gangamin yaki da cutar maleriya da aka gudanar a ma’aikatar lafiya a ranar Asabar.
Yace za’a raba magungunan riga-kafi na maleriya da kayayyakin mata masu ciki da yara kanana da za’a yi wanda hakan zai taimaka ga rage yawan mace-mace daga zazzabin sauran da sauran cutuka daya shafi al’umma.
Ya kara da cewa abune mai muhimmanci su fadakar akan cutar maleriya wanda sama da mutum miliyan 200 da 19 suke kamuwa da ita a Duniya wanda kuma samada kashi 92 na wannan yawan adadi na rayuwane a Afirka wanda kididdiga ta nuna a 2017 kasashe Biyar da suka samarda kashi 50 na cutar daga kasashen Afirka yake ita kanta kasarnan tana dauke da samada kashi 25 na mutanenda suke da cutar da hakan keda mutukar hadari a Najeriya.
Dokta Aminu Ibrahim Tsanyawa yace duba da irin matsaloli da maleriya ke kawowa a kasashe hukumar lafiya ta duniya ya fitoda riga-kafi na cutar duk shekara wannan nada muhimmanci kwarai domin bincike ya nuna cewa samada kashi 75 na maleriya ana iya kareta ta amfani da tsarinda WHO ta bijiro dashi na yin riga-Kafi.
Yace a jihar Kano za’a yi wa yara Miliyan Dubu dari Takwas da talatin da biyar riga-kafin maleriya daga kan yan watanni uku zuwa yan shekaru Biyar a wannan lokaci da za’ayi gangami na riga-kafin .Akwai kuma tsari na kula da mata masu ciki da ake mako-mako a cikin wata uku na shekara wanda akanyi abubuwa dan inganta lafiyar mata masu ciki da yara kanana wanda zai taimaka wajen rage mace-macen mata da yara kanana.
Ya ce, yawanci tsare-tsare da za’a yi a makon dama jihar Kano na samar dasu kyauta za’a inganta shi ne da kara karfafa shi a cikin wannan makon da za’a yi gangami.A bara kashi 92 na yara kanana an samar musu magunguna dan inganta lafiyarsu.
Dokta Tsanyawa ya ce, gangamin za’a fara ne daga Lahadi 11 ga watan 7 har zuwa ran 16 ga watan Yuli dan tabbatarda nasarar cimma tsare-tsare na bada magunguna ga yara da yi musu riga-kafi sannan za’a taba gidajen maganin sauro da auna lafiyar yara kanana dan a tabbatarda basa dauke da wata cuta za’a baiwa mata masu cikin magungunan kandagarki daga maleriya dayin rijistat haihuwa ga yara.
Yace daga cikin tsare-tsaren gangamin akwai wayarda dakan al’umma kan kulada tsaftar jiki data muhalli da bada nono zalla ga yara kanana yan kasa da wata shida da yanda ake amfani da gidan sauro.
Ya yi kira ga magidanta da cewa su kyale mata da yaransu su je wurare da aka kebe dan gudanar da wadannan ayyuka a fadin Kano gaba daya. Ya yaba da irin jajircewa da Gwamnatin Kano take dan bada kulawa ga bangaren lafiya da hakan ke kawo nasarori musamman wajen kauda cutar shan inna wanda yanzu haka jihar Kano da kasa baki daya an kauda ita gaba daya wannan ya samu ne da kokarin Gwamnati da hadin-kan al’umma da sauran kungiyoyin agaji daban-daban.
Ya kuma godewa Gwamna Ganduje bisa irin kulawa da gudummuwa da yake baiwa ma’aikatar lafiya don kula da inganta lafiyar al’umma a Kano.Ya yaba da irin hadin-kai da masarautun Kano guda biyar ke bayarwa dan samun nasarar inganta lafiyar al’umma da kuma abokan hulda da suka hada da hukumar lafiya ta Duniya da UNICEF,Lafiya Project. Gidauniyar Aliko dangote da Gidauniyar Bill da Milinda da sauran masu tallafawa.