Yara Mata Biyu Sun Rasa Ransu A Kududdufi Sakamakon Rashin Ruwan Sha A Jigawa

Daga Abubakar M Taheer

 

A ranar Litinin din satin nan mutanen garin Sabon Gida da ke Karamar Hukumar Kafin Hausa ta Jihar Jigawa sun tashi da alhinin rasuwa yara ’yan mata biyu bayan da su ka rasa ransu a kududdufi lokacin da su ka je diban ruwa.

Wani, wanda ya shaida faruwar lamarin, ya shaida cewa, “lamarin ya faru ne bayan da daya daga cikin yaran ta goyi daya a bayanta, katsam ta fada, inda dayar ta yi ta kokarin dauko ta, amma ina! karfinta ya kare. Daga nan ita ma ta lume. Mun yi kokarin ceto su, amma ina! rai ya yi halinsa.”

Ita ma Mahaifiyar yaran ta bayyana cikin kuka yadda su ka samu labarin rasuwar ’ya’yan nasu da kuma bayyana cewa, wa’adinsu ya yi.

Shi ma Bulaman Garin na Sabon Gida ya bayyana alhininsa kan faruwar lamarin, inda ya kuma bayyana sun dauki duk matakan da su ka dace wajen sanar da jami’an ’yan sanda.

Tuni dai a ka yi jana’izarsu, kamar yadda addinin Islama ya tanadar.

 

Exit mobile version