Connect with us

Nahiyar Afirka

Yara Rabin Miliyan Na Fama Da Yunwa A Libya

Published

on

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yara rabin miliyan ne ke fama da matsananciyar yunwa a birnin Tripoli na kasar Libya sakamakon yakin  da ake ci gaba da gwabzawa tsakanin kungiyoyi masu dauke da muggan makamai.

Hukumar Kula da Ilimin Kananan Yara ta Majaisar Dinkin Duniya, UNICEF ta ce iyalai sama da dubu 1 da 200 sun rasa matsugunansu a cikin sa’oi 48 kadai sakamakon zazzafar fafatawar da ake yi, wanda hakan ya kawo adadin mutanen da suka rasa matsugunansu zuwa dubu 25 kuma rabinsu, yara ne kanana.

Geert Cappelaere, Daraktan Hukumar UNICEF da ke kula da Arewacin Afrika da Gabas ta Tsakiya ya ce, ana ci gaba da daukar yara kanana ana sanya su cikin aikin soji, abin da ke jefa su cikin hadari, ganin yadda ake kashe yaran lokaci lokaci.

Daraktan ya ce ana amfani da makarantu wajen bai wa mutanen da suka rasa matsugunansu mafaka wanda hakan ya haifar da jinkiri wajen bude makarantun yara, yayin da mazauna yankin ke fama da rashin abinci da ruwan sha da kuma wutar lantarki.

Cappalaere ya ce tashin hankalin ya tilasta wa baki da ‘yan gudun hijira cikinsu har da yara kanana barin matsugunansu, yayin da wasu suka fada cikin tashin hankali.

 

 

Up Next

Shan Kwayoyi Ya Kashe Mutum 12 A Nijar A garin Gidan Iddar dake jihar Touha ta jamhuriyar Nijar, mutane 12 ne suka mutu sanadiyar shan muggan kwayoyi da suka hada da wata da ake kira madara. Mutane 12 suka mutu a garin Gidan Iddar dake cikin jihar Touha a kasar Nijar sanadiyar shaye-shayen kwayoyi iri iri da suka hada da wata kwaya mai suna madara. Mutuwar mutanen ya tsorata al’ummar yankin inda suka nemi mahukuntan kasar da su cece su daga wannan bala’i saboda shaye shayen ya kai ga matan aure da ma dattijan gari. Shugaban gundumar Malbaza, wanda kuma shi ne wakilin gwamnati tare da wasu jami’an tsaro da sarkin Dogarawa sun isa garin Gidan Iddar inda suka gana da hakiman garuruwan da bala’in ya shafa. Shugaban gundumar Malbaza Malam Marafa Tankari ya ce za su dauki matakai na ba sani ba sabo game da masu sayar da kwayoyin da masu ajiye masu sayarwa a gidajensu tare da wadanda suke kawosu cikin garuruwansu. Malam Marafa Tankari ya ce daga yanzu doka ce za ta yi aikinta saboda abun da ya faru abun da doka ta hana ne. Domin gudun musguna ma mutane ya sa ba sa shigowa cikin jama’a su yi aikinsu. Yanzu za su yi aikinsu kuma ba za su yadda wani ya taho ya yi masu katsalandan ba. Sarkin Dogarawa ya ce duk wanda ya saukar da masu sayar da kwayoyi a gidansa idan an kama shi, zai dandana kudarsa. Shugaban rundunar tsaro na gundumar Malbaza ya yi kira ga hakiman yankin da su tashi tsaye su yaki wannan muguwar dabi’ar. Ya ce sun san masu aikata laifin amma suna tsoron kada a zarge su da kai ‘ya’yan wasu gidan yari. Dalili ke nan, yasa suna kallon masu laifin suna kyalesu. Ya ce amma yanzu da suka kira hukuma ta shiga za su sa ido su ga irin hobasan da za su yi.

Don't Miss

Kungiyar Timidiriya Mai Yaki Da Bauta A Nijar, Za Ta Shigar Da Kara A Kotun ECOWAS

Advertisement

labarai