Daga Muhammad A. Abubakar, da Ibrahim Ibrahim, Gusau
Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufai ya bayyanawa ’yan Siyasa masu adawa da shi cewa; su guji yin rigima da shi, domin lokacin da tsohon shugaban kasa, Marigayi Umaru Musa ’Yar’adua ya yi rigima da shi, sai ga shi ya mutu.
Gwamnan Jihar Kadunan ya bayyana haka ne a ranar Asabar 16 ga watan Satumbar 2017, lokacin da yake yiwa ’yan siyasa masu adawa da shi gargadi akan da su daina rigima da shi domin tsohon Shugaban Kasa Marigayi ’Yar’adua shi ma da ya yi hakan, mutuwa ya yi.
Jami’iyyar APC a Jihar Kaduna ta fada cikin rikice-rikice da rashin jituwa a tsakanin membobinta irinsu Sanata Shehu Sani, Sanata Suleman Hunkuyi da wasu ‘yan Majalisar Wakilai da suka balle suka ja tunga da Gwamnan. Malam Nasiru El-rufai ya tabbatar da cewa; “Na yi rigima da Shugaban Kasa biyu. Umaru ’Yar’adua ya kare a kabarinsa, shi kuma Shugaban Kasa Goodluck Jonathan ya kare ne a Otueke.”
El-rufai ya ce; “Mu manta da bambance-bambancen dake tsakaninmu, mu yi aiki domin cigaban jam’iyyarmu. Idan ba a shirye kake ka daina rigimar ba, ya kamata ka sani, ni rigimammen mafadaci ne.”
Gwamnan ya tsuguna gaban masu ruwa da tsakin, inda ya nemi gafarar Gundumomi, Kananan Hukumomi, Wakilai na Jihar, da ’Yan Majalisar Wakilai ta Jiha da sauran membobin jam’iyyar ta APC, akan su yafe masa kura-kuransa. Inda ya ce; “Ina rokonku da ku bayyana min kuskuren da na yi muku, domin na nemi gafara. Idan ko har ya wuce yau, babu wanda zan nemi gafararsa.” In ji Gwamnan.
Gwamna El-rufai ya furta wadannan kalamai ne a wurin taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC, wanda aka gudanar a dakin taro na tunawa da Margayi Tsohon Shugaban Kasa Umaru Musa ’Yar’adua, da ke dandalin Murtala a Kaduna.
Taron wanda ba a gayyaci Sanata Hunkuyi ba, amma an yi mamakin ganinsa da ya halarci taron. A lokacin da yake nasa bayanin, Sanata Suleiman Hunkuyi ya bayyana cewa; yana yiwa Nasiru Elrufa’i kallon Babban Yaya ne, amma hakan ba zai hana su samu bambancin ra’ayi a siyasa ba.
Hunkuyi ya ce; “Akwai bambancin tsakanin siyasa da kuma girmamawar da nake yi maka. Idan ka yi kuskure a kowanne gaba a siyasance, ba zan kau da ido na ba, sai na yi maka gyara.” In ji Sanatan.
Shi dai taron an shirya shi ne a wani kokari na ganin an dinke barakar da ta kunno kai a tsakanin manyan ’ya ’yan jami’iyyar APC da ke Jihar Kaduna.
Ofishin mai ba gwamnan Jihar Kaduna shawara akan harkokin siyasa, Malam Uba Sani, ne ya shirya wanannan babban taro, domin sauraren irin ra’ayoyin ’ya’yan Jami’iyyar ta APC dake Jihar Kaduna, domin ganin an sami maslaha.