Zubairu T M Lawal" />

Yaran Da Ke Rayuwa A Sansanin Gudun Hijira Za Su Iya Kamuwa Da Cuta – UNICEF

A bincike na musamman da Kungiyar kula da rayuwar kananan Yara ( UNICEF) ta gudanar dangane da halayen da yaran kanana ke shiga, saboda yanayin rayuwar su ta bangaren abinci da abin sha.
Da yake magana Babban Ma’aikaci na UNICEF, Henrietta ya ce, ceto rayuwar yaran shi ne tallafa masu, da kulawa da halin da suke ciki. Ya kara da cewa, yawancin sansanonin ‘yan gudun hijira a Nijeriya suna bukatar gudummawa.
UNICEF ta ce, Yaran da suke rayuwa a sansanin ‘yan gudun hijira akwai yiwuwar su kamu da cututtuka saboda rashin tsaftataccen ruwan sha.
Wannan bayanin dai ya fito ne a sabon binciken da kungiyar UNICF ta fitar, a inda suka ce yaran na fuskantar barazanar mutuwa sakamakon muhallin da suke rayuwa ba tsaftataccen ruwan sha, kuma babu kyakkyawar walwala.
Binciken ya kara da cewa, sansanin ‘yan gudun hijira ya gurbace, babu tsaftan muhalli, sannan ga cinkoso kuma ba sa samun tsaftatacciyar Iska.
Ta kara da cewa, yara kanana ‘yan kasa da shekaru 15 ke gudanar da rayuwa a wannan gurin.
Ta ce; ya zama wajibi a taimakawa rayuwar kananan yara saboda idan suka kasance a haka to za su fada hadarin rayuwa.
Samar da tsaftataccen ruwan sha da kyakkyawar muhalli zai taimaka wa rayuwar su sosai.
Ba za mu zura ido muna kallo rayuwan yara kanana yana salwanta ba. Halin da suke ciki na rashin matsuguni da fargaban tsaro ya sanya suka gudo suka zo nan.
Bai kamata a ce ana fuskantar matsala makamanciyar waccan ba. Rashin ruwan sha, rashin abinci mai gina jiki da rashin walwala shi ma matsala ce.
Shi ma a nasa jawabin, Babban jami’in UNICEF a Nijeriya, Malam Muhammad ya ce, ruwa yana da mahimmanci a rayuwar dan Adam.
Ya ce; dole ne mu fuskanci matsalolin al’umma a Arewa ta gabas. Ya ce; yanzun haka, sama da mutane milyan uku suke bukatar ruwan sha mai tsafta.
Ya kara da cewa; yanzun haka, dubbannin mutane ke ta kwararowa zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira. Duk da karancin ruwa da abinci da ake fama da shi. Ga kuma karancin muhalli, adadin mutanen da suke zama a sansanonin ya fi karfin sansanonin.

Exit mobile version