Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home SIYASA

Yarfen Siyasa A Ke Yi Wa Gwamnatin Buhari – Mai Aliyu

by Tayo Adelaja
September 13, 2017
in SIYASA
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Muhammad Sani Chinade – Damaturu

Shugaban Kungiyar Makiyaya (Miyetti Allah) na kasa reshen jihohin Arewa maso-Gabas Alhaji Mai Aliyu Usman Biriri, ya kalubalanci mutanen da ke kara rura wutar rikicin makiyaya da al’ummar Kudancin kasar nan da cewar suna yin hakan ne  a kokarinsu na rufe bunsuru da fatar kura don yi wa gwamnatin Muhammadu Buhari yarfen siyasa saboda ya fito daga tsatson Fulani.

samndaads

Shugaban kungiyar makiyayan ya bayyana hakan ne a cikin tattaunawarsa da LEADERSHIP A YAU a garin Damaturu kan hare-haren da ake kai wa wassu yankuna a Kudancin kasar nan tare  yin garkuwa da mutane don biyan kudin fansa ake kuma danganta aikata hakan kai-tsaye ga Fulani makiyaya.

Mai Aliyu ya kara da cewar, abin da masu wannan zarge-zarge kan cewar Fulani makiyaya kada’an ne ke aikata irin wannan ta’asa suka manta shi ne, ai kafin zuwan wannan gwamnati ta Muhammadu Buhari ana samun irin wadannan hare-hare jifa-jifa wani lokacin tsakanin makiyaya Fulani da manoma, wani lokacin kuma tsakanin Fulani makiyayan da wasu kabilu ko kuma barayin shanu wanda  aksari za ka tarar da an fi cutar da makiyayan domin kuwa haka siddan ake bin su daji da wuraren kiwonsu ana kashe su tare da yin awon gaba da dabbobinsu, amma su makiyaya ba su taba dora alhakin hakan ba ga gwamnatin tsohon Shugaban Kasa Jonathan.

Ya ci gaba da cewa, ba wai yana nufin ba a samun kai hare-hare a bangaren makiyaya ba ne, lallai akan samu amma hakan ma takan kasance ne idan har an takale su ko kuma an sace musu dabbobinsu an kuwa sani cewar shi makiyayi kuwa dabbobinsa su ne abokan rayuwarsu. Haka nan, a duk al’umma akan samu bata-gari, don haka a mafi yawa-yawan lokaci bata-garin matasanmu na makiyaya su ma sukan kai harin daukar fansa amma ba wai komai a ce makiyayan ne ke da alhakin hakan ba balle ma a ce wai har kungiyar kan gayyato Fulani daga wasu kasashe irin su Mali, Jamhuriyar Nijar, Senegal da sauransu wai don aikata ta’addanci a cikin kasarmu Nijeriya cewar, wannan abu ne da ba zai taba yiwuwa ba.

Daga nan sai shugaban ya shawarci matasa ‘yan kabilar Ibo da na yankin Neja Delta da ma na wasu bangarorin kasar nan da su kai zuciya nesa bisa maganganunsu na tada  zaune tsaye hakan ba komai ba ne sai kara rura wutar kiyayya a tsakanin ‘yan kasa inda shugaban ya bada misali da kalaman matasa ‘yan kabilar Ibo da suka yi a can baya na bada takamammen lokacin da suke neman makiyaya Fulani a kan su gaggauta barin yankin in kuwa ba haka ba su gamu da fushinsu, a cewarsa hakan ba ita ce mafita ba, domin kuwa Fulani ma ‘yan kasa ne kamar kowa wadanda kan iya shiga kowane yanki na kasar nan su sakata su wala kamar yadda tsarin mulkin kasa na shekarar 1999 ya tanada.

A karshe, ya roki Gwamnatin Tarayya da ta rika daukar matakin ba sani, ba sabo kan irin wannan lamari domin kuwa, sakacin da gwamnatocin baya suka yi hakan ya haifar da halin da ake ciki a yau. Kana ya gargadi mambobin kungiyarsu ta makiyaya da su guji daukar doka a hannunsu.

SendShareTweetShare
Previous Post

Sukar Shugaba Buhari Kan Zuwa Binuwai Tsabar Jahilci Ne -Gwamna Ortom

Next Post

2019 Lokaci Na Ne —Fatima Yawale

RelatedPosts

Har Yanzu Sakkwatawa Ba Su Fara Morar Dimukradiyya Karkashin Mulkin Tambuwal Ba – Umar Lili

Har Yanzu Sakkwatawa Ba Su Fara Morar Dimukradiyya Karkashin Mulkin Tambuwal Ba – Umar Lili

by Nasir Gwangwazo
4 months ago
0

Shugaban kungiyar matasan jihar Sokoto kuma dan gwagwarmayar ganin an...

Wane Ne Hon. Mal Samaila Suleiman (Dujiman Zazzau)?

Wane Ne Hon. Mal Samaila Suleiman (Dujiman Zazzau)?

by Daurawa Daurawa
7 months ago
0

Hon. Malam Sama'ila Sulaiman (Dujiman Zazzau) an haifeshi ranar 03/02/1981,...

Bala Abu Ga Sanata Mandiya: Babu Taimakon Da Ka Yi Wa ‘Yan Gudun Hijirar Faskari

Bala Abu Ga Sanata Mandiya: Babu Taimakon Da Ka Yi Wa ‘Yan Gudun Hijirar Faskari

by Daurawa Daurawa
7 months ago
0

Mataimakin Shugaban jam’iyyar APC yankin Funtua a jihar Katsina, Alhaji...

Next Post

2019 Lokaci Na Ne —Fatima Yawale

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version