Yari Ne Zai Karbi Ragamar Shugabancin APC – Magoya Baya  

Yari

Daga Mahdi M. Muhammad,

Wata kungiyar magoya bayan jam’iyyar APC sun bayyana cewa, duk da rikice-rikicen da ke faruwa a kan shugabancin jam’iyyar a matakai daban-daban, tsohon Gwamnan jihar Zamfara kuma tsohon Shugaban kungiyar Gwamnonin Nijeriya, Alhaji Abdulaziz Yari na shirin zama Shugaban jam’iyyar APC na kasa na gaba daya.

Da suke zantawa da manema labarai a Abuja ranar Lahadi, mambobin sabuwar kungiyar da aka kafa ta ‘Progress for Yari’ (P4Y) sun sanar da shirye-shiryen fara wani gagarumin farmaki kan mummunar labarin karya da ake shirin yiwa Yari, baya ga tona wasu tsirarun manyan ‘yan siyasa da ke bayan irin wadannan ayyukan na bantanci.

Suka kara da cewa, “APC na bukatar Shugaba na kasa kamar Yari wanda zai iya hada kan mutane domin yin nasara a shekarar 2023, domin yana da matukar muhimmanci a lokacin da muke da irin wannan dabi’ar wacce take matukar biyayya ga APC baya ga samun cikakken karfin gudanar da manufofin jam’iyyar da yi mata aiki a dukkan matakai.”

Kungiyar wacce wakilai uku da suka hada da, Jide Kehinde, Umar Adamu da Emeka Nwafor-Ibe suka wakilta, kungiyar ta tabbatar da cewa, dabaru daban-daban da wasu ‘yan kararrakin kotu da ba su hada da wani hukunci mai laifi daya da aka yanke wa dan takarar na su ba, ba abin damuwa ba ne.

Suka ci gaba da cewa, “ganin yadda labarin karya mara tushe da ake ta yadawa ta hanyar yanar gizo da ke nuna cewa an kame gwal na miliyoyin Naira na Alhaji Yari a filin jirgin saman Kotoka, wasu daga cikin magoya bayan Alhaji Yari na Shugabancin kasa sun yanke shawarar tunkarar wadannan makirce-makirce zuwa gaba.”

“Ana kammala shirye-shirye don kaddamar da shirin ‘Progress for Yari’ (P4Y) a duk yankuna shida na yankunan siyasa a duk fadin tarayya, kuma da sannu zaku ji labarinmu da yawa akai-akai,” in ji su.

Suka ce, “ba tare da wata shakku ba, Alhaji Yari ya kasance yana da masaniyar jama’a kuma a koyaushe yana bayyana bukatar ‘yan siyasa su kasance a shirye don ba da sassauci da kuma kiyaye amincin jam’iyya,  kuma babu shakka, kusancinsa da kuma samun dammarsa ga mambobin jam’iyyar a fadin shiyyoyin siyasa shida na kasar nan sun tsayar da shi tuni.”

Suka kara da cewa, “ba kamar ‘yan siyasar da suka fi son makirci ba, Alhaji Yari ya kasance mai son yin sulhu da son zaman lafiya wanda zai zama alheri ga jam’iyyarmu ta APC a matakin jiha da kasa. Bugu da kari, APC na bukatar Shugaba na kasa kamar Yari wanda zai iya hada kan mutane domin yin nasara a shekarar 2023, domin yana da matukar muhimmanci yayin da muke da irin wannan halin wanda yake matukar biyayya ga APC baya ga samun cikakken karfin gudanar da manufofin jam’iyyar da yi mata aiki a dukkan matakai.”

“Dan takararmu baya yin alfahar, kuma ba tare da wata shakka ba yana da babbar dabara da kuma dabaru wajen jagorantar jam’iyyar APC,” in ji su.

Exit mobile version