Yarima Ya Sabunta Rijistarsa Ta APC Bayan Jinkirin Kwana Hudu

Daga Sulaiman Ibrahim

Bayan jinkirin kwana hudu na rashin jituwa, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Ahmad Sani Yarima, a jiya, ya sake sabunta rajistarsa ta zama mamba a jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
An bayyana cewa, Akwai wasu makirce-makirce don kawar da tsohon gwamnan kuma sanata har sau uku daga cikin mambobin jam’iyyar.
Domin rahotanni sun nuna cewa, jiga-jigan jam’iyyar APC an Sabunta musu rajirtarsu a karshen mako yadda shi kuma tsohon gwamna aka ki halartar ta sa.
Yarima ya sabunta rajirtarsa a Gusau, babban birnin jihar Zamfara bayan an sa baki daga fadar shugaban kasa da wasu gwamnoni.
Ya godewa Shugaba Muhammadu Buhari da wasu gwamnoni da suka shiga tsakani don magance rikicin sannan ya yi alkawarin yin aiki tukuru don samun nasarar jam’iyyar a dukkan matakai.

Exit mobile version