Daga Muhammadu Awwal Umar, Minna
A cikin watan shidana bara ne aka zargi Maimuna kishiyar mahaifiyar Buhari Muhammad Awwal Wada da yankewa jaririn dan watanni tara da haihuwa al’aura. Wanda bayan hukumar kula da hakkin yara karkashin jagorancin Barista Mairiam Haruna Kolo ta shiga tsakani dan bin hakkin yaron da daukar dawainiyar kulawa da lafiyar jaririn da taimakon gwamnatin jihar Neja.
Tunda farko kwararrun likitoci na babbar asibitin kwararru na tunawa da Janar Ibrahim Babangida da asibitin kwararru na gwamnatin tarayya, sun yi nasarar yiwa jaririn aikin farko na toshe jijiyoyin da suka samu illa tare da bayyana cewa aiki uku za a yiwa jariri kuma zai warke tare da bada tabbacin za a iya yi mai dashe ta yadda shi ma zai iya anfanar da kanshi wanda ake kyautata zaton zai iya barbarar mace kuma har ta haihu.
Maigirma gwamnan Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya taimaka gaya bayan aikin farkon an sake kai shi asibitin kawararru da ke kasar Amurka dan yin aiki na biyu wanda shi ma an samu nasarar yin aikin bisa taimakon gwamnatin jihar Neja.
Dangane da mai lafin kuwa, Barista Mairiam Kolo tace tun da alkali ya wurga ta gidan hursuna da sunan zaman jiran hukuncin kotu har zuwa yanzu ba wani abu da suka ji game da mai laifin. “ A cewarta kamar yadda alkalin ya bayyana mai laifin, za tai zaman jiran hukunci ne har ranar da hukumar da ke bada shawara akan hukunce-hukunce laifuka DPP ta mika rahotonta.Wannan maganar yanzu wajen shekara daya da watanni ke nan ake yin ta.
A cewarta lallai ba zamu yi sanyin kafa ba.sai hukumar ta tabbatar an hukunta mai laifin.“Ban yi nadama ba kuma mun samun gagarumar nasara sosai domin gwamnatin jiha da kungiyoyi masu zaman kansu sun taimaka dan ceto rayuwar yaron. Hukumata ba za tai kasa a guiwa ba sai ta tabbatar an hukunta wannan matar domin masu hali irin nata su dau darasi.
Ba a hana kishi ba ko a addini akwai kishi, amma ba na halaka mutum ba ko cutar da shi, kuma ma wane irin kishi ne wannan na illata rayuwa ko cutar da yaro kankane”?.