Sagir Abubakar">

Yau A Ke Koma Wa Makarantu A Katsina, Cewar Gwamnatin Jihar

Shirye-shirye sun kamala domin komawa harkokin karatu kamar yadda aka saba a makarantun firamare da sakandire a jihar Katsina.

Wannan ya biyo bayan umarnin da gwamnatin jiha ta bayar na a sake bude makarantun a ranar litinin 5/9/2020.

Kwamishinan kula da ma’aikatar ilimi ta jiha Farfesa Badamasi Lawal Charanchi ya tabbatar da haka yayin zantawa da manema labarai bayan kamala taron majalisar zartaswa na jihad a a ke gudanarwa a kai a kai wanda gwamnan jiha Aminu Bello Masari ya jagoranta.

Advertisements

Kamar yadda yace za a gudanar da darussa ta hanyar bin ka’idojin kare kai daga kamuwa daga annobar cutar corona.

Ya bayyana cewa za a bude makarantun ne da safe da kuma yamma da kuma tabbatar da tsarin yin nesa-nesa da juna a cikin azuzuwa.

Farfesa Badamasi Lawal Charanchi yace yayin da ‘yan aji daya zuwa ukku na firamare zasu zo da safe su kuma ‘yan aji hudu zuwa shidda zasu halarci makarantun da yamma.

Kamar yadda ya ce, dalibai na karamar sakandire daga aji daya zuwa ukku zasu je da safe yayin da daliban babban sakandire zasuje makarantun da yamma.

Ya kuma ce gwamnati ta tanadi dukkanin abubuwan da suka kamata ta kamar samar da wuraren aje ruwa, sabulu da sinadarin wanke hannuwa da kuma na’urar auna zafin jiki domin tabbatar da kariya ga dalibai da malamai.

Kwamishinan ilimi yace hakan labarin yake a makarantun kudi da kuma na kwana.

Ya ce, daliban makarantun firamare dana sakadire zasu kwashe tsawon makwanni ukku domin kawo karshen zangon karatu na biyu.

Don haka, ya yi kira ga iyaye da su bada hadin kai da kuma tabbatar da ganin ’ya’yansu su na da takunkumin rufe baki da hanci a lokacin da zasu tafi makaranta.

 

 

Exit mobile version