Khalid Idris Doya" />

Yau AKe Gudanar Da Zaben Shugaban Kasa A Senegal

Al’ummar Kasar Senegal na shirin kada kuri’unsu a zaben shugaban kasa a yau Lahadi, a zaben da ba kamar yadda aka saba ba, shugaba mai ci Macky Sall ba ya fuskantar adawa mai tsananin gaske.
Macky Sall dai na ikirarin cewa yana da yakinin lashe zaben a zagaye na farko. Sall dai na shugabanci a kasar da malaman addinin ke da tasiri wajen zabar shugaba tun daga shekara ta 2012, inda a yaanzu zai fafata da ‘yan takara uku kacal a zaben na yau Lahadi 24 ga wannan wata na Fabarairu da muke ciki. Ana dai yi wa kasar ta Snegal kaallon abin koyi wajen zaman lafiya da fahimtar juna a nahiyar Afirka baki daya.
Yanzu haka bayan rage sanya wa kasar Nijeriya ido wajen ganin yaz aben shugaban kasarta zai kasance, yanzu ido ya sake juyawa kan kasar ta Senigal kwanaki guda ne tsakanin zaben Nijeriya da Senigal, kawo yanzu masu fashin baki suna kan nazartar yaddaz aben na yau zai gudana a kasar ta Senigal

Exit mobile version