Bayan da aka kammala buga wasannin gasar Zakarun Turai zagaye na biyu da ya kunshi kungiyoyi 16 da suka fafata a junansu, a yau hukumar dake kula da gasar kofin nahiyar turai zata raba jadawalin kungiyoyin da suka rage a gasar ta bana.
Sai dai yayin wasannin da aka karkare a ranar Laraba 17 ga watan Maris, Bayern Munich ta samu nasara kan kungiyar kwallon kafa ta Lazio da 2-1, sai Chelsea wadda ta doke Atletico Madrid da ci 2-0.
Tun a ranar Talata kuma an fafata wasanni tsakanin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid wadda ta doke kungiyar Atlanta da ci 3-1 sannan kuma Manchester City ma ta doke kungiyar kwallon kafa ta Borussia Monchengladbach da ci 2-0.
A wancan satin kuwa daya gabata kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta fice daga gasar ne bayan canjaras 1-1 data buga da kungiyar Paris Saint German saboda a wasan farko PSG din ce ta samu nasara da ci 4-1 a gidan Barcelona.
Sai wasa tsakanin Liverpool da RB Leipzig, wasan da Liverpool ta samu nasara itama da ci 2-0 bayan da a wasan farko shima Liberpool din ce ta samu nasara daci 2-0 a gidan kungiyar ta Leipzig ta kasar Jamus.
Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta fita daga gasar ne duk da cewa ta samu nasara da ci 3-2 akan kungiyar kwallon kafa ta FC Porto sai dai a wasan farko Porto din ce ta samu nasara da ci 2-1 a kasar Portugal.
Sai kuma kungiyar kwallon kafa ta Dortmund wadda itama ta samu nasara akan kungiyar Sevilla ta kasar Spain bayan da a wasan farko Dortmund din ce ta samu nasara a wasan da aka fafata a gidan Sevilla a kasar Spain.
Kungiyoyi 8 da suka samu nasarar tsallakawa zuwa zagayen wasan kusa da kusa da na karshe na kwata final, sun hada da Chelsea da Bayern Munich da Manchester City da Liverpool da PSG da Real Madrid da Borussia Dortmund da kuma kungiyar kwallon kafa ta FC Porto.
A yau Juma’a hukumar kwallon kafa ta Turai UEFA za ta fitar da jadawalin kungiyoyin da za su kara da juna a zagayen na kwata final sannan taron fitar da jadawalin kuma zai gudana ne a birnin Nyon dake kasar Switzerland.