Yau Ce Ranar Arfah: Musulmi Miliyan Biyu Za Su Sauke Farali

Hukumomin Kasar Saudiyya sun fid da sanarwar cewa ana sa ran Musulmi miliyan biyu ne za su sauke farali a hajjin bana, ciki har da sama da mahajjata dubu 55 daga Nijeriya.
Aikin na wannan shekarar zai fara ne a yau yayin da mahajjatan za su yi tururuwa domin hawan Arfah.
Ranar 9 ga watan Zhul-Hijja rana ce da addinin Musulunci ya ayyana a ranar Arfah, inda miliyoyin musulmi suke taruwa a filin Arfah domin sauke daya daga cikin shika-shikan ibadar hajji.
Ranar Arfah na daya daga cikin ranakun da ke tattara miliyoyin al’umman da suke da bambancin launin fata, harshe, da kuma matsayi na rayuwa a wuri daya.
Addinin Musulunci ya zo da cewa, a wannan tsauni na Arfah ne Kakanmu Adam da Hauwa’u suka hadu bayan an sauko dasu daga Aljannah.
Ana kwadaita wa musulmi yin azumin nafila a wannan rana domin su dace da falolin da ke cikinta.
Tun shekaran jiya aka fara jigilar maniyyatan Nijeriya zuwa rumfunansu da aka tanada a Muna, wanda aka kare a daren jiya Lahadi. Hukumar Kula da Alhazan Nijeriya (NAHCON) ta bayyana cewa sama da Maniyyata 55,000 za su kasance yau a filin Arfah domin sauke farali.

Exit mobile version