Connect with us

LABARAI

Yau ‘Discourse Forum’ Ta Ke Bukin Tunawa Da Galadiman Kano, Tijjani Hashim

Published

on

A yau 29 ga watan Satumba, 2018 ne wata kungiya mai suna ‘Dicourse forum’ ta ke bukin tunawa da shekaru 4 da rasuwar Marigayi Galadiman Kano, Alhaji Tijjani Hashim.

Kungiyar ta fitar da jawabin bukin tunawar ne a wata takardar wacce Shugabanta, Huzaifa Dokaji ya rabawa manema labarai a Birnin Kano.

Takardar ta bayyana irin nagarta da mutuncin da Marigayi Galadiman Kano yake da shi a idon Kanawa, da kuma irin tasirin da yayi a rayuwar dimbin jama’an da ya gina yayin da yake raye.

Huzaifa ya bayyana cewa; “Mun shirya wannan taron manema labarai ne domin tunawa da zagayowar shekaru hudu da rasuwar Marigayi Galadiman Kano, Tijjani Hashim. Shekaru hudu ne masu cike da alhini da rashi ne shugaba adili.

“Galadima Tijjani Hashim na daya daga cikin nagartattun ‘ya’yan Jihar Kano wadanda suka tasirantu a rayuwar al’umma. Ya yi kaurin suna wurin yin amfani da damar da ya samu don taimakawa talakawa.” inji shi

Takardar ta kara da cewa, Galadiman Kano ya fara tasiri ga rayuwar Matasan Arewa ne tun bayan da ya shiga cikin ‘yan majalisar arewa a shekarar 1956, lokacin yana dan shekaru 24 a duniya. Wanda a lokacin aka yi mishi shaidar daya daga mutanen da suka kasance tare da Sardauna a lokacin da ake cikin tsanani. Saboda tsabar dagiyarsa da kafiya akan sai an kyautatawa marasa galihu ne Sardauna ya yi masa lakabi da ‘Internal trouble’.

“A shekarar 1966 ne Galadima Tijjani Hashim ya taka rawa a muhimman abubuwa uku, lokacin yana memba na ‘yan majalisan arewa, mai wakiltar gundumar Sumaila, kuma Sakataren ma’aikatar cikin gida, sannan kuma a lokaci guda Mukaddashin Kwamishina a yankin Kabba. Wadannan halayen kwarai da dagiya na daga cikin abubuwan da suka sa, mu matasa muke ganin akwai abin koyo daga wannan bawan Allah” inji kungiyar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: