Yau Gwamnoni 17 Za Su Gudanar Da Babban Taro A Legas

Daga  Khalid Idris Doya

A yau Litinin ne Gwamnoni 17 da suka fito daga Kudu maso yamma da kuma kudu maso gabas, da kudu maso kudu za su hallara a birnin Legas domin tattaunawa a kan muhimman batutuwan da suka shafi ƙasar nan, da kuma ƙara ƙulla alaƙa mai tsafta a tsakanin su gwamnonin.

Wannan taron da za su yi shi a yau, an shafe sama da shekaru 12 da yin irinsa, sai kuma a yau wanda za su tattauna domin fayyace muhimman babututuwa.

Sanarwar taron na gwamnonin ta fito daga sakataren gwamnatin jihar Legas, Mista Tunji Bello wanda ya raba ga manema labaru. Sanarwa ta ce taron gwamnonin jahohin Legas da takwararsa na Akwa Ibom ne suka ɗauki nauyin gudanarwa.

Taron gwamnonin dai zai zai ba da damar su cimma matsaya guda ɗaya a cewar sakataren, matsayar a kan batutuwa kamar su yaƙi da masu fashi da makami, garkuwa da mutane da kuma batun nan na raba madafun iko, kana da kuma tattaunawa kan batun sake fasalin Nijeriya.

Exit mobile version