Yau Jam’iyyu 35 Ke Fafatawa A Zaben Gwamnan Ekiti

Dubun dubatar masu kada kuri’a ke dandanzo yau a rumfunan zaben Jihar Ekiti domin raba gardama a tsakanin ‘yan takarar jam’iyyu 35 kan wanda zai zama musu sabon Gwamnan jihar.
Zaben gwamnan jihar ta Ekiti yana da matukar muhimmancin gaske bisa yadda ake daukar sa a matsayin zakaran gwajin dafin zabukan da za a yi na kasa baki daya a watan Fabarairun badi idan Allah ya kai mu.
A jiya Juma’a, Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana cewa ta kimtsa tsaf domin gudanar da zaben na yau.
Babban kwamishinan hukumar a Jihar Ekiti, Farfesa Abdulganiy Raji ya fada wa manema labarai cewa an raba komai da komai na kayan aikin zaben a sassan kananan hukumomin jihar 16, kana ma’aikatan hukumar da jami’an tsaro sun kammala shirin fara aikin zaben.
Kwamishinan ya bayyana cewa hukumar ta yi kyakkyawan shirin gudanar da zaben, domin hatta yadda aka yi rabon kayan zaben ba a boye ba an fito da komai baro-baro a fili ta hanyar wata na’ura da aka makala a motocin hukumar da ke raba kayan zaben wadanda suke nuna wuraren da motocin ke bi har zuwa wuraren da aka tura su. Ya ce kai tsaye daga ofishinsa ana kallon komai ta wani katon akwatin talabijin.
Ya bukaci masu kada kuri’a su fito kwansu da kwarkwata su yi zabe cikin kwanciyar hankali da lumana, kasancewar an tsaurara tsaro sosai domin tabbatar da komai ya gudana cikin dadin rai.
Farfesa Abdulganiy ya ce jam’iyyu guda 35 ne ke fafatawa a zaben daga cikin jam’iyyu 40 da suka nuna muradin shiga zaben tun da farko.
A halin da ake ciki kuma, Basarake Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwasi ya nuna rashin jindadinsa da abubuwan da suka faru a Jihar Ekiti a shirye-shiryen gudanar da zaben na yau Asabar.
A cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na fadar Basaraken ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis da ta gabata, an ruwaito Basaraken yana bayyana bacin ransa a yayin da Jakadan Birtaniya a Nijeriya, Mista Paul Arkwaright ya ziyarci fadarsa a Ile Ife.
Basaraken ya ce idan aka samu tashin-tashina a zaben na Ekiti, abin zai shafi sauran jihohi makota.
“Abin da na ji ma kunnena yana faruwa a Jihar Ekiti a lokacin shirye-shiryen zaben ban ji dadinsa ba a matsayina na uban kasa. Mun gaji da rikici, ba mu da bukatarsa a kasar Yarabawa. A duk inda ake tashe-tashen hankula ba a samun cigaba sabanin wurin da ake zaman lumana da zai rika samun bunkasa. Ni da kaina, na ja kunnen matasan Ekiti kan cewa kowa ya zauna lafiya kafin zaben, da lokacin gudanarwa da kuma bayan kammalawa saboda rayuwarsu za ta yi kyau idan sun fahimci irin baiwar da Allah ya yi musu.
“Wajibi ne matasa su yi watsi da yadda ake amfani da su wajen tayar da rikicin siyasa da ke sa su mutuwa a banza, saboda su ma da kansu a kwana a tashi wata rana za su zama gwamna ko shugaban kasa ma baki daya”.
Basaraken ya yaba wa Gwamnatin Birtaniya bisa taimakon Nijeriya da take yi wajen tabbatar da zaman lafiya kasar, kana ya nemi Jakadan ya kara yaukaka zumuncin kasuwanci a tsakanin Nijeriya da Birtaniya domin amfanin juna.
Da yake nasa tsokacin, Jakada Arkwright wanda shi ne mai sanya ido na Birtaniya a zaben na Ekiti, ya yi kiran gudanar da sahihin zabe na gaskiya da adalci kuma cikin kwanciyar hankali.
Idan ba a manta ba dai, shugabannin jam’iyyar PDP sun yi zanga-zanga zuwa Majalisun Dokoki na Kasa domin nuna bancin ransu kan tarwatsa gungun magoya bayansu da suka fito wani gangamin da ‘yansanda suka ce ba su nemi izinin yi ba.

Exit mobile version