Musa Muhammad" />

Yau LEADERSHIP Ke Karrama Gwarazanta Na 2019

A halin da a ke ciki dai yau ne a ke gudanar da gagarumin bikin nan da a ka jima a na sanarwa, inda kamfanin buga jaridun LEADERSHIP ke gabatar da taro, don gudanar jawabai tare da karrama wasu fitattun ’yan Nijeriya wadanda su ka yi fice a harkokinsu na yau da kullum a 2019, wadanda su ka hada da ma’aikatan gwamnati, ’yan siyasa, masu zaman kansu, kamfanoni da dai sauransu.

Shi dai wannan taron, kamfanin namu yana gudanar da shi ne duk shekara, inda ya ke zakulo wadannan mutane da muka ambata a sama, a karrama su don a kara masu kwarin gwiwar ci gaba da abin da suke yi. Wannan bikin da za a gudanar, duk da ana yinsa ne a 2020, amma na 2019 ne, wadanda suka yi fice ne a shekarar ta 2019 ake yi wa wannan karramawa.

An zabi mashahuran ‘yan Nijeriya biyu, wadanda suna daga cikin wadanda za a ba kyautar, an kuma sa su cikin ajin mutanen LEADERSHIP na shekarar 2019, su mashahuran ‘yan kasuwa ne da suka hada da, Chief Femi Otedola da kuma Shugaban Hukumar shirya jarabawar zuwa manyan makarantu ta kasa, Farfesa Ishak Olarewaju Oloyede.

Da yake bayani akan su matakan da aka dauka da Jaridar ta amince da su, Manajan Daraktan kamfanin LEADERSHIP, Mu’azu Elazeh ya bayyana cewar Otedola ya yi nasara ne wajen samun kyautar ta mutumin shekarar 2019, an shiga wani sabon babi ne, wanda kuma lokaci ne ya yi yadda za a canza akalar al’amarin, domin akwai wani lokaci wanda idan aka yi la’akari da kaddarorin sa na iya sa ba za a zabe shi ba wajen samun kyautar. Amma saboda yadda yake taimaka wa al’umma ne ya sa haka ya sa aka Cigaba daga shafi na zabe shi.

Sauran wadanda za a ba nau’o’in kyaututtuka na wannan shekarar sun hada da Gwamnoni, wadanda kamfanin ya aminta da irin kokoarinsu na ciyar da jiharsu gaba, kamar su Muhammad Badaru Abubakar na Jigawa, Ben Ayade na Cross Riber, Bello Mohammed Matawalle na Zamfara, da kuma Ahmadu Umaru Fintiri na Adamawa, su ne suka kasance Gwamnonin LEADERSHIP na shekarar 2019.

Sai kuma karamin Minista a ma’aikatar albarkatun man fetur, Timipre Silba, shi ne wanda ya samu kyautar dan siyasa na shekarar 2019, yayin da kuma kyautar harkar Banki ta je ga Shugaban Bankin bunkasa Afrika (AfDB), Dokta Akinwumi Adesina.

Shi kuma Bankin Access Bank shi ne ya samu kyautar Banki na shekara, yayin da kuma kyautar Hukuma ta kasance ne a hannun Hukumar hana fataucin dan Adam ta (NAPTIP).

Ita kuma kyautar mutumin Hukumar gwamnati, wanda kuma babban jami’i kuma Shugaba na Hukumar kula da asusun manyan makarantu, Farfesa Elias Suleiman Bogoro, sai kuma Shugaba kuma babban jami’i na Aiteo Group, Benedict Peters, shi ne wanda ya samu kyautar mutumin harkokin kasuwanci na shekara.

Akwai kuma tsohon Shugaban Hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasa, Dokta Maikanti Kachalla Baru, shi ne wanda ya lashe kyautar shugaba na bangaren Hukumomi na shekara.Sauran nau’o’in kyaututtukan su ne na kayayyakin amfani na shekara , Tiamin Rice; da kuma kamfanin Komfuta, ko kuma fasahar kamfan ICT na shekara, shi ne Main One; sai kuma Kamfanin E-Commerce na shekara, OPay; harkar sadarwa na shekara, Huawei Technologies Company Limited, da kuma wanda ya fi burgewa na shekara Airtel.

Daga karshe kuma akwai kyautar da ake ba matashi na shekarar 2019, wanda yarin yarinyar nan da ke hannu Boko Haram ta samu, wanda kuma ita ce ake duk shekara ake ba wannan kyauta, tun lokacin da aka sace su wato Leah Sharibu; sai kuma Burna Boy, wanda shi ne zakaran bangaren mawaka na shekara, sai kuma kyauta ta bangaren wasanni, wacce kulob din wasan kwallon kwando na mata ya lashe.Game da manyan bakin da ake sa ran za su halarci bikin na bana kuwa, su hada da Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Muhammad Namadi Sambo, wanda kuma shi ne zai shugabanci taron da aka yi wa taken “ Tasirin rufe iyakoki akan tattalin arzikin kasa”.

Haka nan ma Shugaban Hukumar ‘Nigeria Sobereign Inbestment Authority (NSIA),’ Uche Orji, shi ne wanda zai yi jawabi, tare da Ministan babban birnin tarayya, Alhaji Muhammad Musa Bello, wanda kuma shi ne mai masaukin baki.

Bugu da kari kuma Gwamnan jihar Yobe, Mai-Mala Buni; da kuma Ministan ayyuka na musamman, Sanata George Akume; Etsu Nupe wanda shi ne shugaban Sarakunan jihar Neja, Alhaji Yahaya Abubakar; Sarkin Potiskum, Alhaji Umaru Bubaram da Deji na Akure, Oba Aladetoyinbo Aladelusi duk amsa za su halarci taron.

Exit mobile version