Connect with us

LABARAI

Yau Majalisa Za Ta Tattauna Kan Kasafin Kudin INEC

Published

on

Akwai yiwuwar Majalisun tarayya za su rage yawan kudin da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa take bukata a cikin kasafin kudin da aka aikewa Majalisun, kasantuwa wasu abubuwa da aka rika maimaita su a cewar kwamitin hadin gwiwar.
Kamar yadda wakilinmu ya nazarto a ranar Asabar, binciken sa ya nu na, kafin zaman kwamitin hadin gwiwa kan zaben na Majalisun biyu wanda aka shirya zaman sa a ranar 27 ga watan Agusta, wakilan kwamitin sun fi mayar da hankalin su ne kan karban kasafin kudin da hukumar ta aike masu na Naira bilyan 189.2.
Kasafin kudin hukumar da Shugaba Buhari ya aike wa da majalisun shi ne Naira bilyan 143. Hakan shi ya kawo kiki-kaka a tsakanin wakilan kwamitin tun kafin tafiyar su hutun Sallah, kan ko su yi aiki ne da kasafin da hukumar zaben ta aike masu da shi ko kuma wanda Shugaban kasan ya aike masu da shi.
Sai wata majiya ta kwamitin ta shaida mana cewa, akwai yiwuwar wanda hukumar zaben ta aike da shi ne kwamitin zai yi aiki da shi, amma akwai yiwuwar ya rage shi kasantuwan wasu abubuwa da aka maimaita a cikin sa.
Wani babba ya shaida wa wakilinmu cewa, sun gano an maimaita abubuwa masu yawa a cikin kasafin kudin, musamman kan abin da aka ware ma ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro.
Majiyar ta kara da cewa, da zaran kwamitin ya dawo zaman na shi a ranar Litinin, zai fara ne da fitar da abubuwan da kwamitin ya gano an maimaita su, ta hanyar gayyato shugabannin hukumomin tsaron da abin ya shafa domin su kare sabon kasafin kudin da suka gabatar.
Majiyar ta ce, tana yiwuwa shugabannin hukumomin tsaron da za a gayyato su bayyana a ranar ta Litinin, ko kuma a shawarta ranar da za su bayyana a gaban kwamitin.
“Matsalan a nan ita ce, akwai yiwuwar kwamitin na hadin gwiwa ya kammala ko ya kasa kammala zaman na shi a ranar ta Litinin, wanda ya danganta ne da hanzarin da shugabannin hukumomin tsaron suka yi na zuwa su kare sabbin abubuwan da suka shigar a kasafin kudin na INEC.
“Misali, tilas ne mu guji hanzarin baiwa hukumar ‘yan sanda Naira bilyan 6 a kasafin kudin na INEC, bayan kuma can a wani wajen an kebe wa hukumar ta ‘yan sanda wasu Naira bilyan 6.
Da aka so jin ta bakin shugaban kwamitin bincike da kasafin kudi na majalisar wakilai ta tarayya, Mista Timothy Golu, ya tabbatar da cewa, kwamitin hadin gwiwar ya gano maimaicin da aka yi din, kuma zai warware komai a ranar ta Litinin.
Golu, wanda wakili ne kuma a cikin kwamitin majalisar kan harkokin zabe da Jam’iyyu, ya tabbatar da masaniyarsa kan gayyatan shugabannin hukumomin tsaron da za a yi.
Wakilin namu ya yi kokarin jin ta bakin shugabar kwamitin majalisar, Aisha Dukku, wanda bai sami nasarar yin hakan ba.
Wakilin namu ya kuma fahimci cewa, ayyukan kwamitocin zaben na majalisar za su iya tilasta yiwuwar sake dawowar zaman majalisar a watan Satumba.
Daya daga cikin wakilan kwamitin ya shaida wa wakilinmu cewa, batun ranar dawowa zaman majalisa ma ba ta taso ba, domin tilas ne kwamitocin su kammala ayyukan su kafin majalisar ta zauna.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: