Yau Ne Za A Yanke Hukunci Kan Karar Jam’iyyar PDP

A yau Talata 30/1/2018 ne ake sa ran kotu  za ta yanke hukunci a kan karar da jam’iyyar PDP ta jihar Kano ta shigar kan hukumar zabe mai zaman kanta a gaban wata kotu don a yi mata fassarar sayen fom da ake yi na Hukumar zabe. Mataimakin dan takarar Shugabancin Karamar Hukumar Takai a inuwar jam’iyyar PDP a jihar Kano, Malam Yakubu Husaini Takai ne ya bayyana haka ga manema labarai.

Ya ce suna son fassarar ya zama wajibi ne ga dan takara kafin ya yi takara sai ya sayi fom na Hukumar zabe ko yana da ikon yin takara ba tare da ya sayi wannan fom ba?

Ya yi nuni da cewa sun ga Hukumar zabe ta kasa ba ta taba saida fom ba a duk zabukan da take yi. Don haka ne suka yarda duk abubuwan da aka yi a baya bisa kuskure ne a zamanin mulkin Shekarau da lokacin Kwankwaso.

Malam Yakub Takai ya ce ba daidai ba ne sun gano kuskure a ce kuma su je su ci gaba da yi, duk da cewa akwai cikin ’yan PDP da suka soma sayen fom din, amma aka dakatar da su har sai jam’iyya ta ce an daidaita tsakanin jam’iyya da KANSIEC lokacin da kotu ta yanke hukunci da suke sa rai yau Talata 30 ga watan nan za ta yi kan abin da ya dace kan Shari’ar.

Ya ce fom da ake Magana, ana so ne APC kadai ta samu, an ce Gwamna ya saya wa dukkan ’yan takara a APC. Kananan jam’iyyu ba wacce ta je ta saya, su ma ba su aka yi, su PDP laifin me suka yi? “In dai ba tsoro suke jin na yin takarar da mu ba, ko yau aka ce mu janye kara za a ba mu fom mu shiga zabe, za mu janye mu shiga zabe,” in ji shi.

Malam Yakub Husaini ya yi nuni da cewa gwamnatin APC ta Kano tsoron zaben Kananan Hukumomi take ji da PDP, don in dai zabe za a yi na dangwala kuri’a a kirga, to jam’iyyar PDP sai ta ci Kananan Hukumomi da Kansiloli mafiya rinjaye a jihar Kano.

 

Exit mobile version