Connect with us

RAHOTANNI

Yau Sarkin Bauchi Ke Cika Shekara 10 A Karagar Mulki

Published

on

A yau Alhamis, 30 ga Yuli, 2020, ne Mai Martaba Sarkin Bauchi, Alhaji Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu, ke bikin ciki shekaru 10 cif a kan karagar mulki Masarautar ta Bauchi mai cike da dimbin albarka.
Wakilinmu ya shaido cewar bikin ya zama wani gagarumi ga al’ummar jihar da Masarautar lura da cewa Sarkin na da shekaru goma a kan mulki, wanda kuma Sarkin shine Sarkin Yakin Daular Usmaniyya.
An samu habakar zaman lafiya, cigaban tattalin arziki, hadin da dinkewar baraka a karkashinsa lamarin da ya kara masa Martaba da kima a idon al’ummar masarautar.
Sarkin Rilwanu, mai shekaru 50 a duniya, ya zama Sarkin Bauchi ne bayan da Malam Isa Yuguda a shekarar 2010 sa’ilin da ke kujerar Gwamnan Jihar Bauchi ya nada shi bayan fafata nema da wasu ‘ya’yan marigiyi tsohon sarki da ‘ya’yan masarautar suka yi.
Tun bayan nadinsa a matsayin Sarki ake kara samun zaman lafiya da fahimtar juna musamman ga mambobin masarautar Bauchi da al’umman jihar.
A yayin bikin da aka gudanar na cikar shekara 10 an zabi gudanar da muhimman addu’o’i domin neman karin dafawa daga wajen Allah hadi da neman tabbatuwar zaman lafiya mai daurewa.
Wakilinmu ya nakalto cewa tsohon gwamnan jihar Bauchi, Isa Yuguda ya amince da nadin Dakta Rilwanu a matsayin sarkin Bauchi ne daga cikin ‘yan takara mutum 20 da su ke nemi sarautar tun a shekarar 2010.
Dakta Rilwanu shine Sarkin Bauchi na 11, wanda ya kasance daya daga cikin ‘ya’ya 16 na marigayi tsohon Sarki Alhaji Sulaiman Adamu.
LEADERSHIP A YAU ta nakalto cewa an haifi Dakta Rilwanu ne a ranar 14 ga watan Oktoban 1970 a garin Bauchi, ya halarci makarantar Firamare ta Kobi da ke kwaryar Bauchi a tsakanin shekarar 1976 zuwa 1982, ya kuma tafi sakandarin gwamnati da ke Toro daga shekarar 1982 zuwa 1987, daga nan kuma ya zarce zuwa kwalejin kimiyya da fasaha mallakin gwamnatin jihar Bauchi (ATAP) daga shekarar 1991 zuwa 1995 wanda ya samu shaidar ilimin malanta ta koyarwa (NCE), ya kuma zarce zuwa jami’ar ATBU da ke Bauchin domin samun shaidar digiri na farko a bangaren kimiyyar gine-gine (Bsc in building technology) daga 1996 zuwa 2001.
Mai martaba Sarkin na Bauchi ya yi aiki da hukumar ‘Nigeria Port Authority’ daga shekarar 2002 zuwa 2006, kafin ya nada shi a matsayin sarkin Bauchi ya kuma yi aiki da Nigeria Sao-Tome da PJDA.
Yanzu haka jama’a na ci gaba da taya Sarkin da masarautar Bauchi murna bisa wannan gagarumar nasara na ganin shekara 10 a bisa milkin masarauta cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali.
Advertisement

labarai