Daga Abdulrazak Yahuza, Abuja da Abdullahi Moh’d Sheka, Kano
A yau Juma’a mun shiga sabuwar shekarar Musulunci ta alif dubu daya da dari hudu da talatin da tara (1439) bayan hijirar cikamakin Annabawa, Manzon Rahama, Annabi Muhammad (SAW).
Shigar sabuwar shekarar tana nuna an yi bankwana da shekarar da ta gabata, kuma a halin yanzu za a fuskanci abubuwan da za a aiwatar a sabuwar shekarar ta 1439.
Kamar yadda tarihi ya bayyana, shekarar Musulunci ta hijira ba an fara kirgata ba ce a lokacin da aka yi hijira daga Makka zuwa Madina, sai bayan wafatin Annabi (SAW) a zamanin Sayyidina Umar (RA) aka fara.
A bana, Makka ta fara kirgar sabuwar shekarar ne daga jiya Alhamis a yayin da mu kuma Nijeriya muka fara a yau Jumma’a. An samu banbancin ne saboda mu a nahiyarmu akwai sarkakiya game da tsayuwar watan a ranar Laraba, shi ya sa yau Juma’a ta zamo daya ga watan Muharram.
Akwai bukatar kara wayar da kan al’umma a kan shigowar sabuwar shekarar domin kowa ya san cewa kara kusantar kabari ake a kullu yaumin.
A halin da ake ciki kuma, Kakakin Majalisar Dokin Jihar Kano Alhaji Abdullahi Ata, ya bukaci al’ummar musulmi a fadin kasar nan da su kara kaimi wajen addu’ar dorewar zaman lafiya a kasa baki daya. Kakakin ya nuna bukatara hakan ne cikin jawabin da ya yi ga manema labarai a Kano, kuma daraktan yada labaran majalisar dokokin Jihar Kano Alhaji Ali Bala Kofar Kudu ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis da ta gabata cikin sakon taya murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci 1439 bayan Hijira.
Abdullahi Ata ya bukaci al’ummar Kano da su ninka soyayyar juna tare da kokarin kare hakkin abokan zamansu ba tare da la’akari da bambance-bambancen kabila ko addini ba. Ya ce watan Almuharram wanda ya zama watan farko a sabuwar shekarar Musulunci ta 1439 bayan da Hijarar Ma’aiki (SAW) daga Makka zuwa Madina, lokaci ne na tuna abubuwan da suka gudana ba maida hankali wajen tarukan holewa da bukukuwa ba. Saboda haka ya hori jama’a da su kauce wa abubuwa marasa kyau da suka gudana a shekarar da ta gabata tare da himmatuwa wajen kyautata al’amura cikin wanann sabuwar shekara.
Ya ci gaba da cewa, Majalisar Dokokin Jihar Kano da Gwamnatin Kano za su ci gaba da tabbatar da wanzar da zaman lafiya tsakanin al’ummun da ke Jihar Kano, sannan a tabbatar da wani ko wasu ba su wargaza hadin kan al’umma ba. Haka nan, ya ce gwamnatin na daukar duk matakan da suka kamata don samun nasara, saboda haka ya bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da dukkan hadin kan da ake bukata ga gwamnti da jami’an tsaro.
Dadidadawa, ya ce Majalisar Dokokin Jihar Kano za ta ci gaba da kyautata hadin kai, gaskiya da zaman lafiya tsakanin duk wanda ke wannan jihar mai albarka da ma kasa baki daya. Tare da cewa, idan aka dubi irin ci gaban da aka samu a Jihar Kano da ma kasa baki daya, akwai bukatar kara matse kaimi wajen yawaita addu’a don samun karin ci gaban da ake bukata. Sannan ya bukaci jama’a da a kara yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari addu’ar samun dorewar lafiya don ci gaba da gudanar da ayyukan da aka alkaurata wa jama’a.