Yau Take Sabuwar Shekarar Musulunci Ta 1439

Daga Abdulrazak Yahuza, Abuja da Abdullahi Moh’d Sheka, Kano

A yau Juma’a mun shiga sabuwar shekarar Musulunci ta alif dubu daya da dari hudu da talatin da tara (1439) bayan hijirar cikamakin Annabawa, Manzon Rahama, Annabi Muhammad (SAW).

Shigar sabuwar shekarar tana nuna an yi bankwana da shekarar da ta gabata, kuma a halin yanzu za a fuskanci abubuwan da za a aiwatar a sabuwar shekarar ta 1439.

Kamar yadda tarihi ya bayyana, shekarar Musulunci ta hijira ba an fara kirgata ba ce a lokacin da aka yi hijira daga Makka zuwa Madina, sai bayan wafatin Annabi (SAW) a zamanin Sayyidina Umar (RA) aka fara.

Shekarar ta hijira tana da watanni 12 wanda a cikinsu, akwai guda hudu da Allah ya haramta yaki a cikinsu, sai kuma wasu muhimmai da ake gabatar da ibadodi na addini a cikinsu. Kamar yadda tarihi ya nuna, an haifi Manzon da ya sanar da duniya bakidaya Musulunci a watan hudu (Rabi’ul Auwal). A cikin wata na tara ake gabatar da ibadar Azumin Ramadan, sai bikin Sallar Idil Fidir da ake yi a wata na goma (Shauwal) da kuma fara shirin zuwa Hajji tun daga Shauwal har zuwa Zhul-Hajji, tare da gabatar da Sallar Idin Layya ga Musulmin da ba su tafi Aikin Hajji ba. Kowane wata a cikin watannin Musulunci yana da albarkar da Allah ya yi a cikinsa.

A bana, Makka ta fara kirgar sabuwar shekarar ne daga jiya Alhamis a yayin da mu kuma Nijeriya muka fara a yau Jumma’a. An samu banbancin ne saboda mu a nahiyarmu akwai sarkakiya game da tsayuwar watan a ranar Laraba, shi ya sa yau Juma’a ta zamo daya ga watan Muharram.

Akwai bukatar kara wayar da kan al’umma a kan shigowar sabuwar shekarar domin kowa ya san cewa kara kusantar kabari ake a kullu yaumin.

A halin da ake ciki kuma, Kakakin Majalisar Dokin Jihar Kano Alhaji Abdullahi Ata, ya bukaci al’ummar musulmi a fadin kasar nan da su kara kaimi wajen addu’ar dorewar zaman lafiya a kasa baki daya. Kakakin ya nuna bukatara hakan ne cikin jawabin da ya yi ga manema labarai a Kano, kuma daraktan yada labaran majalisar dokokin Jihar Kano Alhaji Ali Bala Kofar Kudu ya raba wa manema labarai a ranar Alhamis da ta gabata cikin sakon taya murnar shigowar sabuwar shekarar Musulunci 1439 bayan Hijira.

Abdullahi Ata ya bukaci al’ummar Kano da su ninka soyayyar juna tare da kokarin kare hakkin abokan zamansu ba tare da la’akari da bambance-bambancen kabila ko addini ba. Ya ce watan Almuharram wanda ya zama watan farko a sabuwar shekarar Musulunci ta 1439 bayan da Hijarar Ma’aiki (SAW) daga Makka zuwa Madina, lokaci ne na tuna abubuwan da suka gudana ba maida hankali wajen tarukan holewa da bukukuwa ba. Saboda haka ya hori jama’a da su kauce wa abubuwa marasa kyau da suka gudana a shekarar da ta gabata tare da  himmatuwa wajen kyautata al’amura cikin wanann sabuwar shekara.

Ya ci gaba da cewa, Majalisar Dokokin Jihar Kano da Gwamnatin Kano za su ci gaba  da tabbatar da wanzar da zaman lafiya tsakanin al’ummun da ke Jihar Kano, sannan a tabbatar da wani ko wasu ba su wargaza hadin kan al’umma ba. Haka nan, ya ce gwamnatin na daukar duk matakan da suka kamata don samun nasara, saboda haka ya bukaci jama’a da su ci gaba da bayar da dukkan hadin kan da ake bukata ga gwamnti da jami’an tsaro.

Dadidadawa, ya ce Majalisar Dokokin Jihar Kano za ta ci gaba da kyautata  hadin kai, gaskiya da  zaman lafiya tsakanin duk wanda ke wannan jihar mai albarka da ma kasa baki daya. Tare da cewa,  idan aka dubi irin ci gaban da aka samu a Jihar Kano da ma kasa baki daya, akwai bukatar kara matse kaimi  wajen yawaita addu’a don samun karin ci gaban da ake bukata. Sannan ya bukaci jama’a da a kara yi wa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari addu’ar samun dorewar lafiya don ci gaba da gudanar da ayyukan da aka alkaurata wa jama’a.

Exit mobile version