Yau Za A Buga Wasan Karshe Na Gasar Kofin Zakarun Turai

A yau Asabar za a fafata wasan karshe na gasar Kofin Zakarun Turai tsakanin kungiyoyin Tottenham da Liverpool. Wasan zai gudana ne a garin Madrid na kasar Sipaniya. Liverpool na fatan lashe kofin karo na shida, yayin da Tottenham kuma ke harin lashe kofin a karon farko a tarihi.

A bara Real Madrid ce ta haramta wa Liverpool lashe kofin a Kiev. Kocin Liverpool Jurgen Klopp ya ce sun koyi darasi daga rashin nasarar da suka yi a hannun Real Madrid a bara.

Kocin Tottenham kuma Mauricio Pochettino ya ce tsallakewa zuwa wasan karshe a gasar cin kofin zakarun Turai, wani al’amari babba da zai iya faruwa da kulub din a tarihi.

Rabon da Liverpool ta lashe wani kofi tun 2012, tsawon shekara bakwai, yayin da Tottenham kuma tun 2008,  shekara 11 da suka gabata.

Fafatawar lashe babban kofin na Turai na da matukar muhimmanci ga kungiyoyin biyu na Ingila. Karon farko ke nan da kofin gasar zai tafi Ingila bayan shekara 11. An shafe shekaru kofin na zuwa Sipaniya.

Exit mobile version