Yau Za A Gwabza Tsakanin Arsenal Da Man UTD A Gasar Firimiya

Daga Sulaiman Ibrahim,

Yau Manchester United ke maraba da abokiyar hamayyarta Arsenal a filin wasa na Old Trafford don fafatawa a gasar Firimiya, ranar Alhamis.

Red Devils ta samu maki daya a wasan da ta buga na karshe da kungiyar dake jagorantar ragamar gasar Firimiya, Chelsea yayin da Gunners ta doke Newcastle United da ci 2-0.

Arsenal ba ta yi rashin nasara ba a wasanninta shida na karshe da ta yi da United – a gasar da aka buga sau uku a jere.

A wannan wasa na tsakiyar mako, kunnen doki zai maida Arsenal sama da West Ham zuwa ta hudu a teburin yayin da United za ta iya tsallakewa zuwa matsayi na shida ko ma kasa da matsayi na 14 in aka shata.

Exit mobile version