Mukhtar Anwar" />

Yaudarar Mutanen Karkara Da Alkawuran Boge Na ‘Yan Siyasa

Masu karatu barkan mu da sake haduwa a wannan makon. Idan ba ku manta ba, kafin waiwayen da muka yi game da tarihin zaben shugaban kasa a Nijeriya a makon da ya gabata – wanda muka yi saboda zaben da aka so gudanarwa a ranar Asabar ta makon jiya abin bai yiwu ba – muna tattaunawa ce a kan wasu al’amuran da suka wakana a zabukan Nijeriya na baya. A wannan makon za mu ci gaba daga inda muka tsaya tare da duba yadda ‘yan siyasa a zaben 2007 suka yi wa al’ummomin yankunan karkara alkawuran boge.
Yayin da ake daf da fara aiwatar da Zaben Shekara ta 2007, sai ya kasance, wasu ‘Yan Koren Gwamnati tare da hadin-bakin Malaman Zabe, na shiga yankunan Karkara gami da yi wa jama’a alkawuran karya kawai don samarwa da jam’iyyar gwamnati tulin magoya baya.
Wadancan ‘Yan koren na gwamnati, sun rika neman al’umar Karkara Manyansu da Yaransu, da su fito su yi rijistar zabe. Tare da girba karyar cewa, ta hanyar yin wannan rijista ne kadai, gwamnati za ta yi tunanin kawo musu ayyukan cigaba a garuruwan nasu.
(Daily Trust, April 9, 2007).
An tabbatar da cewa, an samu a Kauyen Denga na karamar hukumar Kurfi ta jihar Bauchi, inda gwamnati ta tura wasu Wakilanta zuwa garin, suna masu fadawa jama’a cewa, su fito manyansu da yaransu (wadanda ba su isa yin zabe ba) su yi rijistar zabe. Sun kara da cewa, idan suka bar wadannan yara nasu suka yi rijista, gwamnati za ta samar musu da tataccen ruwan-sha tare da gina musu hanyoyi masu kyawo. (Ibid).
Malam AbdulRahman Jalo mazaunin garin Denga, ya tabbatar da cewa, wasu jami’an aikin rijistar zabe da jami’an gwamnati, sun zo garin nasu suna masu fada musu cewa, ta hanyar yin wannan rijista ne kadai, gwamnati za ta auna ta ga shin, sun cancanci samun ayyukan cigaba a yankin nasu?. Sai dai Jalo ya ce, ko kadan ba su dauki wannan magana ta mutanen da wani muhimmanci ba, kasantuwar an sha zuwa da kwatan-kwacin irin wadannan alkawura amma ba a cika musu.
Ba laifi ne ba, a yi wa jama’a alkawarin za a gabatar musu da ayyukan cigaba yayin kamfen, sai dai bisa wace hujja ko dalili ne zai sa, malaman rijista da wasu jami’an gwamnati za su hade-kai wuriguda tare da gabatarwa da jama’a irin wadannan alkawura? Koko su ce, duka manya da yara a fito a yi rijista in ji gwamnati? A ina ne ma ake da hujjar da za ta sahalewa Malamin Zabe fitowa fili ya nuna bangaren jam’iyyar da yake marawa baya yayinda ya fito aikin yi wa jama’ar gari rijista?.
Ga Malamin rijistar zabe, Masana sun fitar masa da wata ka’ida abar la’akari, yayin gabatar da aikin nasa. Masanan sun ce;
“Dole ne Jami’in rijistar zabe ya kaucewa duk wani abu da zai sa a zarge shi, har ta kai ga tunanin yana marawa wani bangare baya ne. Saboda haka ne ma yasa, ba a daukar Ejan na wata jam’iyya ko na wani Dan Takara aikin yin rijistar zabe. Hatta ma wani mutumin da aka taba kamawa da aikata laifin zabe ko aikata manyan laifuka irin su, rashin gaskiya ko cin amana, ba za a dauke shi yin aikin rijistar zabe ba” .
(A. A. Ujo, 2002 : 68-69).
Ko ba a fada ba, za a ga cewa irin wadancan ka’idoji da aka zayyana game da wadanda za a dauka aikin rijistar masu zabe, an gindaya su ko shimfida su ne domin son ganin an tsarkake hanyar daga abubuwa na almundaha, son zuciya, zargi, son kai da ma dukkanin wani abu da zai taimaka wajen haddasa rikici ko samun rashin fahimtar juna a tsakanin masu zabe.
Wani abu mai kama da almara shi ne, kwanaki kalilan da irin wadancan alkawura na boge da jami’an gwamnati ke bin yankunan Karkara suna yi wa jama’a, kwatsam! kuma sai ga ma’aikatan Masaka ta Kaduna sun fito, su da Matayensu sama da dubu goma sha biyu, tare da yin zanga-zangar neman hakkokinsu. Suna masu yin kira ga jumlar gwamnonin Arewacin wannan Kasa, na ko dai a ba su hakkokinsu, ko kuma su ki fita yin zaben da za a yi cikin kwanaki hudu masu zuwa.
(Daily Trust, April 12, 2007).
Kasar da wanda yai aiki ya tsofar da kuruciyarsa da karfin jikinsa ga aiki mai wahalar gaske, gwamnati ba ta damu da ta kyautata rayuwarsa ko ta iyalansa a lokacin da yake aikin da bayan ya yi ritaya. Yaya a hankalce za a yarda cewa irin wadannan gwamnatoci za su cikawa mutanenmu na Karkara irin wadancan holokon alkawura na yaudara, alhali ga wadanda ke musu aiki dare da rana an banzatar da su, ashe sai wanda ke zaune can a gefe ne cikin Karkara za a bi har can kurya a kyautatawa?.
Wasu Wurare Da Gwamnatoci Suka Tafka Magudi A Zaben Na Shekarar 2007
Zargi kala-kala ya yawaita, inda ake korafin wasu manyan jami’an gwamnati da kanana, wajen yunkurin tafka magudin zabe, cikin wannan zabe na Shekarar 2007. A kan hanyarsu ta lashe zabe ta ko wane irin hali.

A Jihar Katsina, 2007
A cikin jihar ta Katsina, ya tabbata cewa, bayan kammala gudanar da Zaben Gwamna, jam’iyyun adawa sun yi wani taron manema labarai, inda suka yi Allah-wadai da sakamakon zaben da aka fitar, bisa la’akari da wasu abubuwa na kauce ka’idar zabe da suke zargin bangaren gwamnati da aikatawa.
An yi wancan gangamin taro ne a Ofishin jam’iyyar AC na jihar ta Katsina, karkashin jagorancin Dan Takarar kujerar gwamna na jam’iyyar, Dr Bugaje. Daga abubuwan da dandazon ‘Yan Jam’iyyun na adawa ke korafi a kai, sun hadar da;
i -Hadin-baki da aka samu karara tsakanin jami’an tsaro da malaman zabe da kuma wasu jami’an gwamnati, a lokacin gudanar da zabukan. Sun ma fadi sunayen wadancan jami’an na gwamnati wadanda suke a matakin jiha da matakin kananan hukumomi.
ii -Sun yi karin haske game da wasu akwatuna da aka kama makare da kuru’un boge jibge ciki, wadanda tuni an yi dangwale a cikinsu.
iii -Sun ma fadi tarin wasu kuru’un boge tuli da aka yi yunkurin shigo da su cikin Kasar nan daga Jamhuriyar Niger.
(Daily Trust, April 16, 2007)
A Jihar Akwa Ibom, 2007

‘Yan takara bakwai (7) na kujerar gwamna daga jam’iyyun adawa sun yi taro, inda suka nuna rashin gamsuwarsu game da sakamakon zaben da hukumar zabe ta jihar Akwa-Ibom ta shelanta a zaben na Shekarar 2007.
(Daily Trust, April 17, 2007)
Gungun wadancan ‘Yan takara 7, sun hadar da; James Iniama na jam’iyyar AC; Edet Inwang na jam’iyyar ADC; Group Capt. Samuel Enwang na jam’iyyar ANPP; Pastor Cyrill Itahowo na jam’iyyar CPP; Obong Samuel Atang na jamiyyar DPP; Dr Ekeng Anam Ndu na jamiyya LP, sai kuma Obong Dr Chris Ekpenyon, na jam’iyyar PPA.
‘Yan takarar, sun fadi nau’ikan magudin zabe iri-iri gami da yi wa dokokin zabe hawan-kawara da aka yi wajen gudanar da zaben. An tabbatar da samun wasu gidaje talatin da uku (33), inda gungun wasu mutane suka dukufa dangwalen kuri’a ba-ji-ba-gani, alhali a can tashar zabe ne kadai a ka halasta yin irin wancan dangwale na kuri’a sabanin cikin gidajen jama’ar gari.
An tabbatar da cewa, cikin wadancan gidaje 33 da aka samu a na irin wancan haramtaccen dangwalen kuri’a, har da gidan Kwamishinan Kudi na jihar. Sannan, ba kawai suna yin dangwalen kuri’a ba ne, a’a, akwai miyagun makamai rike a hannunsu.
Alhaji Isyaku Ibrahim BOT/PDP Ya Koka
Duk da kasancewar Alhaji Ibrahim guda cikin ‘Yan Kwamitin Amintattu na jam’iyya mai mulki a matakin kasa, hakan bai hane shi kyamatar Zaben Shekarar 2007 da aka gabatar ba, tare da fassara zaben a matsayin wanda ba ingantacce ba.
“…Hakikanin gaskiya na girgiza tare da bacin rai dangane da abinda ya faru a ranar Asabar (ranar da aka gabatar da zabukan)”, in ji Isyakun, sannan ya kara da cewa, duba da abubuwan suka faru na rashin bin ka’ida a zabukan da aka gudanar cikin duka fadin wannan Kasa, hakan na nuna kwata-kwata babu wani darasi da muka koya daga abubuwan-ki da suka afku cikin wannan Kasa a baya. Ko shakka babu, babu kanshin gaskiya cikin wadannan zabuka da aka gudanar, kuma a fili yake cewa wadannan
zabuka ba sahihai ne ba.
(Daily Trust, April 17, 2007).
Abu na gaba da za mu tashi a kai shi ne, rawa abar zargi da Jagororin Siyasa suka taka a Zaben na Shekarar 2007.
Daga Mugunyar Rawar Da Jagororin Siyasa Da Mabiyansu Suka Taka A Zaben Shekarar 2007
Ga fahimtar wannan Marubuci, yawan kashe-kashe da ake samu a tsakanin ‘Yan Siyasa, da sunan wata hanya abar amfani don kai wa ga matakin nasarar lashe zabe, ya fi kowane irin magudin zabe a bayan Kasa muni. Idan kana maganar muhimmancin yi wa jam’iyyu rijista ne, ko yin rijistar zabe, ko kirkira tare da bin dokokin zabe, ko ba da damar yin kamfen na siyasa, ko aikace-aikacen hukumar zabe, da ma duk wani abu da Mutum zai fadi ko zai hararo dake da jibi da harkar zabe, duka don Mutum ne ake yin su. Da babu Mutum a bisa doron kasa, duka sunansu TARKACEN ISKA. To kuma sai aka wayigari a na kashe shi wannan MUTUMI da ya kere su muhimmamci Duniya da Lahira. To shin, ina ke nan a ka dosa? Zuwa ga shiriya ne ko bata?.
Kisan gilla na yankan kauna ya kasance ruwan -dare cikin Shekarar Zaben 2007. Ya faru cewa, wasu kashe-kashen na ta’addanci, an aiwatar da su ne gabanin ranakun zabe, wasu kuwa an yi su ne a ranakun zaben. Wai duk dai don a sanawa jam’iyya kaza nasarar lashe zabe!!!. Da daman bincike ya tabbatar da cewa, jagororin SIYASA ne ke daukar nauyin irin wadancan asarar RAYUKA da ake samu na “YA”YAYEN MARASA GALIHU A KASA.
Kamar yadda mai kasa kaya ke sanya mabanbanta farashi bisa hajarsa, shi ma aikewa da wani MUTUM lahira da sunan siyasa, wani abu ne dake da farashi hawa-hawa, gwargwadon kimar wanda za a kashe, gwargwadon kima ko kaurin ‘Yan mutsabban da za a dunkule a bai wa masu zuwa zartar da kisan.
(Daily Trust, April 2, 2007).
Rashin girmama dokokin jam’iyya da murgude su gwargwadon yadda za su amfani mai mulki, wajen biyan bukatarsa ta kashin-kai, ko murguda sakamakon zabe na cikin gida na jam’iyya bisa son zuciya, da kin yin biyayya da jam’iyyun siyasar ke yi wa umarnin Kotu da makamantan su, duka wadannan miyagun ta’adodi sun faru a wurare mabanbanta dake da alaka da wannan zabe na Shekarar 2007.
(Daily Trust, April 4, 2007 & Daily Trust, April 13, 2007).
Mai karatu ya sani cewa, duk wata halayya ta tafka magudin zabe da Jagororin Siyasa da Mabiyansu suka aikata cikin Zaben Shekarar 2003, za a ga sun maimaita kwatankwacinta ko ma sama da ita a wannan Zabe na Shekarar 2007.
Gabanin kutsawa cikin-abubuwan kaico da suka afku cikin wannan zabe, wadanda wadancan jagororin siyasa da mabiyansu suka jaza faruwar ta sun, za mu dan waiwayi baya, game da siyasar daba da ta’addanci da ta nemi zama ruwan dare gabanin zaben 2003 da bayansa. Daga nan, sai mu dora da waccan ta’adata cigaba da kisan-mummuke da aka rika samu a tsakanin ‘Yan Siyasar, a wannan Zabe na 2007. Alhali bayan kai wa ga samun nasarar lashe zabuka, za a ga irin wadancan Karnukan Farautar ‘Yan Siyasa da ake amfani da su wajen aikewa da Mutane Lahira, a na watsar da su ne. Sai su rika bin kwararo-kwararo, ba su ga tsuntsu ba su ga tarko, can kuma Lahira a na jiran su karaso su amshi sakamakonsu da Hannun Hagu.
Za mu ci gaba a mako mai zuwa da bayani a kan ire-iren kisan gillar da suka dabaibaye siyasarmu ta baya. Allah ya kai mu da rai da lafiya, amin.

Exit mobile version