Leadership News Hausa
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership News Hausa
No Result
View All Result

Yaushe Amurka Za Ta Dakatar Da Tsoma Baki Cikin Harkokin Cikin Gidan Sauran Kasashe?

by
1 year ago
in DAGA BIRNIN SIN
2 min read
Yaushe Amurka Za Ta Dakatar Da Tsoma Baki Cikin Harkokin Cikin Gidan Sauran Kasashe?
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram
ADVERTISEMENT

Labarai Masu Nasaba

Manyan Jami’an Diflomasiyya Na Kasashen Sin Da Amurka Sun Tattauna Ta Wayar Tarho

Kara Cudanya Maimakon Katse Hulda Mafita Ce Ga Tattalin Arzikin Duniya

Daga CRI Hausa

Amurka ta ce, ta farfado da shawarwari da kasar Iran jiya Alhamis a birnin Vienna na kasar Austria, a wani kokari na ceto yarjejeniyar nukiliyar Iran wadda aka daddale a shekara ta 2015. Tuni, jagoran addinin Iran Ayatollah Seyyed Ali Khamenei ya bayyana cewa, in Amurka tana son dawowa yarjejeniyar, kamata ya yi ta soke tukunkumin da ta sanyawa kasarsa.
Bayan yakin duniya na biyu ya zuwa yanzu, Amurka ta dade tana tafiyar da manufar shiga sharo ba shanu cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, ciki har da kai harin soja, da sanya takunkumi, da tunzura masu tada rikici. Wato Amurka tana yin duk wani abun da za ta iya don nuna babakere a duk fadin duniya baki daya.
Bayan da Joe Biden ya hau karagar mulkin Amurka, ya sha nanata cewa zai maida hankali sosai kan batun hakkin dan Adam a cikin harkokin diflomasiyyar kasar. Wato Amurka tana fakewa da batun hakkin dan Adam don tsoma baki cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, alamarin da ya haddasa rikicin zubar da jini a sassa da dama a duniya. Tambayar a nan ita ce, idan wata kasa ta rasa ikon mulkin kai, ta yaya za ta kare hakkin dan Adam a kasar?
A cikin sanarwar da aka fitar a wajen babban taron Majalisar Dinkin Duniya da aka yi a shekara ta 1965, an ce, bai kamata wata kasa ta tsoma baki cikin harkokin gidan sauran kasashe ba duk hujjar da take da ita. Kada wata kasa ta yiwa sauran kasashe barazana ta hanyar daukar matakan siyasa da soja da kuma tattalin arziki don sauran kasashe su mika wuya. Bugu da kari, sanarwar ta ce, bai kamata wata kasa ta hura wutar rikici da tallafawa ayyukan kifar da gwamnatin sauran kasashe ba. Amma, ita Amurka, ta yi duka.
Duk da cewa annobar COVID-19 tana ci gaba da yaduwa a duniya, Amurka ba ta dakatar da ayyukan ta na sanyawa sauran kasashe takunkumi ba, abun da ya illata hadin-gwiwar kasa da kasa wajen yaki da annobar, da tsananta matsalar jin-kai a duniya.
Rashin yin shisshigi cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe, babbar manufa ce a cikin kundin tsarin mulkin MDD, wadda ta samu amincewa daga kasa da kasa. Yaushe Amurka za ta daina tsoma bakinta cikin harkokin cikin gidan sauran kasashe? (Mai Fassara: Murtala Zhang)

Like this:

Like Loading...
SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamnatin Buhari Ta Yi Abubuwa Da Dama Na Cigaba A Nijeriya -Alhaji Amadu Haruna Zago

Next Post

An Bude Ofishin Kungiyar Gamayyar ‘Yan Kasuwa A Karamar Hukumar Bakori

Labarai Masu Nasaba

Manyan Jami’an Diflomasiyya Na Kasashen Sin Da Amurka Sun Tattauna Ta Wayar Tarho

Manyan Jami’an Diflomasiyya Na Kasashen Sin Da Amurka Sun Tattauna Ta Wayar Tarho

by
14 hours ago
0

...

Kara Cudanya Maimakon Katse Hulda Mafita Ce Ga Tattalin Arzikin Duniya

Kara Cudanya Maimakon Katse Hulda Mafita Ce Ga Tattalin Arzikin Duniya

by CMG Hausa
14 hours ago
0

...

Jakadan Sin Ya Yi Kira A Bada Fifiko Wajen Bunkasa Ci Gaban Yankin Sahel

Jakadan Sin Ya Yi Kira A Bada Fifiko Wajen Bunkasa Ci Gaban Yankin Sahel

by Abdulrazaq Yahuza Jere
14 hours ago
0

...

Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabi Ga Taron Ministocin Wajen Kasashe Mambobin Kungiyar BRICS

Xi Jinping Ya Gabatar Da Jawabi Ga Taron Ministocin Wajen Kasashe Mambobin Kungiyar BRICS

by CMG Hausa
15 hours ago
0

...

Next Post
Gas

An Bude Ofishin Kungiyar Gamayyar ‘Yan Kasuwa A Karamar Hukumar Bakori

Domin bayar da talla ko neman ƙarin bayani a tuntuɓe mu a: +2348039216372

  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us | English Edition | Fashion Magazine | Business News

© 2022 Leadership Media Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2022 Leadership Media Group .

Go to mobile version
%d bloggers like this: