Abdurrahman Aliyu">

Yaushe Arewa Za Ta Gane Amfanin Ilimi?

Rayuwar Duniya cike ta ke da kalubale, duk da fadi tashi da kiraye-kirayen da ake ta yi kan ilimantar da ‘ya’ya mata da ba su damar samun ingantaccen ilimi musamman na Firamare da karama da babbar Sakandire, amma duk da haka wasu na fuskantar tarnakin rayuwa da samun cikas ga cikar wannan kuduri da aka cimmawa.
Bincike ya bayyana har yanzu kashi talatin da uku 33 na mata ke samun shiga Makarantun boko a Nijeriya, kuma mafi yawancinsu ba su samun damar kammala ko karamar sakandire, ake cire su a yi masu aure, sakamakon girma jiki da kuma samun mazajen auren da wasun su ke yi da wuri, da sauran dalilai na Mahaifan ‘ya’ya.
Daga cikin kalubalan da mata ke fuskanta a kwai na al’adu wadda ita ce take masu tarnaki ga barin su samu ilmin zamani da ake son kowace diya mace ta samu, wadda a ganin wasu mahaifan na ganin bai da wata fa’ida a ilmantar da mace, domin in ta samu ilimi ba za ta yi biyayyar aure ba. Kuma ma tana iya rasa manema, har ta kai ta zama abin da Hausawa ke kira da Sabagiji. Al’adu su na ganin macen da samu ilimin boko ana ma ta kallon na musamman a cikin al’ummar da take rayuwa a cikinta, na zargi da aibanta da nuna wa samari isa da jin kai, Musamman a cikin wasu kauyikan.
Kazalika, su kansu yaran su na wa ilmin boko kallon kamar wani kalubale a gare su domin mafi yawancin su ba su daukar sa da mahimmanci, su na ganin cewa in da saniyar gaba ta sha ruwa nan ta baya za ta sha, ba sai sun bata lokacin su ga karatun ba, domin dai somin tabi ne kawai za su yi su a cire su.
Duk da wannan kallon da al’adu da zamantakewa ke wa ilimin boko, amma bai fidda a’i a ga rogo ba, ga kalubalen rayuwar ‘ya’ya mata ba, domin har yanzu akwai abin na nan, dan za a cire yarinya daga makaranta in ta samu miji an mata aure nan ma wani sabon ilimin ne, domin wasu kan fada hannun mazaje masu tafiya ci rani a wasu jihohi, wadda in sun dawo karkarar su tamkar wasuAlhadawa, da haka za su burge tsaffin kauyukan nasu, musamman mata har su kwadaitu da san ba su ‘ya’yan su aure, kuma da zarar an yi auren wasu in sun sa gaba ba su kara waiwayo baya, sai su share wata biyar zuwa bakwai ba su leko gida ba. Iyakar su da iyalan duk bayan sati biyu su turo masu katin 1500, wadda in su toro masu, matan su sayar 1200, da ita za su yi bukatocin tayuwa ta yau da kullum da ta hada da sayen abinci, ruwa, man shafawa da yar hoda. Ba batun sutura ake ba, domin ‘yar wadda aka yi a lokacin biki sai a shafe haihuwa uku ba a kara ba, ba a batun noma, domin dama kudi ake turowa, yanzu kuwa an yi iyali kudin da ake turowa ta katin waya sun hana turo kudin noma. Akwai ma wanda ba su da damar turo katin wayar, sai dai in wasu za su taho gida su aiko wasu ma kan share fiye sa shekara biyu, sannan a aiko. Wasu matan tun da suka yi aure basu taba wata cif da mazajen su ba a gida. Saboda irin dogon zangon da mazajen kan yi wajen nema, shi ke haifar da kowamar matan gidajen iyayen su. Wato abin nan, da Bahushe ke kyama kan tabbata, na ka sayar da Akuya ta dawo tana ci ma danga, sai mace ta share dogon lokaci a gidan su, sai idan mijin ya zo ta ke komawa dakin ta.
A wani kalubale kuwa sai in mace ta samu juna biyu, bai cimaka ba zuwa duba lafiyar uwa da abin da ke jikinta, haka za a yi ta laulayi har lokacin da Allah zai fitar da abin da zai fitar da abin da ke ciki, wadda ta samu ta sauka lafiya tai barka, sai kuma na kalubalen fafutukar abin da za ta dan hada a uwar hanjinta ta samu ruwan mamar da za ta shayar da abin da ta haifa, domin mafi akasari mazajen ba su nan ake haifuwar, ba kuma wani tanadi suke mata ba, sai dai uwar diyar tai ta kai koma wajen ciyar da ‘yarta, dangin miji kuwa sun kokarta su leko barka, da dan tarfin gero a tafarfara, domin su riga sun raba jiha tun lokacin da ya bar bada kudin noma, haka kowace ‘yar barka za ta dan leko ta kama gabanta don ba cimaka. Har dai a samu a yi suna.
Raino wani kalubale ne, domin babu cima balle abin da aka haifa, ya samu kwari da ingantaciyar lafiya, ba kuma ta zuwa asibiti ake ba, da cikin ma ba a je awo ba, balle ya zo duniya.
A na cikin haka batun karin aure ya ke tasowa, da zaran mazaje sun ga an yi masu haihuwa kuma abokanan su mazauna gida na ta kara aure sai suma su shiga fagen kara aure, kwatsam sai kara jefo ma shi wata mai tsautsan, ita ma da an samu sati biyar da amarci zuwa shidda ya bar su ya kama gabansa. Ita ma ta bi layin gadon matsalolin da duk waccan ke fuskanta da ga mijin, sai dai kuma gara ita a bangaren iyayen mijin domin ita ta farin za ta shiga tasku da kara kwomadewa kamar dan giginya, musamman in daukin angonci ya sa mijin ya dan leko gida bayan tafiyar sa da wata biyu ko uku.
Irin wadannan mata kan zama tsofaffin dole da kurciyar su, kan zama kazamai na ki da kari, wanda ba su iya kula da gyara kansu balle muhallinsu, uwa uba ma abin da suka haifa, cututtuka kan yi masu kawanya basu san suna da su ba, inda kuma tsautsa daga rani mazajen kan taho masu da tsarabar wasu cututtukan. Ya kamata iyaye su yi karatun ta natsu su fuskanci wadannan kalubale da sukan taimaka wajen jefa a ‘ya’yansu mata a ciki. Ta hanyar kaucewa al’adun da suke masu tarnakin, da har suke nakasa rayuwar ‘ya’yansu da su, domin yanzu duniya ta ci gaba, al’umma suna watsar da duk ruko da wata gurguwar al’adar da ka hana masu cigaban rayuwar su da ta ‘ya’yansu. Domin zamanin nan sai ka gyara naka duniya ke son shi, sannan kuma su tallafi kudurorin gwamnati na tallafawa rayuwar ‘ya’yansu da ilmin boko, ta hanyar barin yaran su suma ilimin da ake bukatar kowace diya mace ta samu, dan da shi ne ake samun sinadarin inganta rayuwar zamantakewar miji da mata da ‘ya’yan da za su haifa, har ma da tsara tattalin arzikin da iya rage fuskntar kalubalen rayuwa.
Kazalika, da ilmi ne ake sanin makamar inganta lafiyar mutum da ta iyalai da kuma sanin yadda ake zama da iyayen miji da danginsa da ma makwafta baki daya.
Ya kamata matasa su rige barin garuruwansu su na tafiya ci rani, dan su ma a nasu garuruwan suna da hudodin arzukin da su iya dogara da su, wanda har al’umma za ta yi alfahari da su, kuma zaman su gida zai ba su damar samun ilmin boko wanda zai taimaka masu kwarai wajen inganta tattalin arziki da makamar rayuwa, dama Hausawa kan ce ‘Yunkurinka Makomarka’.

Exit mobile version