Tun bayan samun ’yancin kai daga Turawan mulkin mallaka, mu ke fama da rikice-rikicen addini da na kabilanci har ma da na siyasa a Arewancin Najeriya.
Rikicin Maitatsine shi ne rikicin addini na farko mafi muni da Arewancin Najeriya ta fuskanta a jamhuriya ta biyu karkashin mulkin marigayi Alhaji Shehu Usman Aliyu Shagari. Tun daga wancan lokacin da a ka yi rikicin Maitatsine, an yi ta samun rikice rikicen addini da na kabilanci daban-daban, kamar daga Arewacin zuwa kudanci zuwa gabashin kasar.
A farkon shekarar 1980 ne a ka yi rikicin Maitatsine a jihar Kano, wanda daga bisani ya bazu zuwa Yola da Maiduguri da Bauchi da Gombe, inda a ka yi asarar rayukan dubun-dubatar mutane da su ka hada da Musulmai da Kirista. Bayan wannan, rikice-rikicen da su ka fi muni sun hada da rikicin Zangon Kataf na jihar Kaduna a shekarar 1992 tsakanin Hausawa da Katafawa, wanda daga bisani ya rikide ya koma na addini.
A wannan rikicin shi ma an yi asarar rayuka da dukiyoyi masu dimbin yawa. Sai kuma rikicin Shagamu na jihar Ogun a watan Yulin shekarar 1999 tsakaninYarabawa da Hausawa, biyo bayan kisan wata mata Bahaushiya da wata kungiya mai suna (Oro) ta yi, inda su ka ce ta keta ka’idarsu. Kashe-kashen da a ka yi wa Hausawa a Shagamu ya sa a Kano ma matasa sun dauki fansa kan Yarabawan da ke zaune a can.
Sai kuma a watan Nuwamban shekarar 1999, inda wani rikicin kabilanci ya sake barkewa a unguwar Ajegunle a jihar Legas tsakanin kungiyar OPC (Oodua People’s Congress) da ta matasan kabilar Ijaw.
Bayan kwantar da wannan rikicin a watan Disambar wannan shekarar, an sake samun wani barkewar rikicin kabilancin a kasuwar Mile 12, tsakanin kungiyar OPC da Hausawa, bisa dalilan shugabancin kungiyar masu sayar da doya a kasuwar, wato Shukura Yam Sellers Association, wacce kusan Hausawa ne ke rike da shugabancinta, inda aka yi asarar rayuka sama da dari biyu tare da kone kasuwar kurmus.
Bullo da tsarin shari’ar Musulunci a wasu jahohin Arewacin kasar shi ne ya yi sanadiyar rikicin addini a jihar Kaduna a watan Fabrairun 2000, inda nan ma aka yi rikici tsakanin Musulmai da mabiya addinin Kirista wadanda suka nuna rashin amincewarsu ga amfani da shari’ar Musulunci a jihar. Rikicin wanda ya bazu zuwa garuruwan Kachiya da Zariya da sauransu, shi ma ya haddasa asarar daruruwan rayuka da dukiyoyi masu dimbin yawa.
Bayan wannan rikicin na Kaduna an samu makamancinsa a jahohin Sokoto da Barno musamman ma a garin Damboa na jihar Barno.
An fara samun rikici a Jos tun daga shekara ta 2001, wanda asalinsa na siyasa ne tsakanin ‘yan asalin yankin Pilato da kuma Hausa/Fulani dake zaune a can, kafin daga bisani ya rikide ya koma na addini da kabilanci, kuma ya kasance daya daga cikin manyan rikice-rikicen da aka samu a Najeriya. Rikincin Jos na faruwa ne tsakanin Hausa/Fulani Musulmai da kuma ‘yan yankin na Pilato wadanda akasarinsu mabiya addinin Kirista ne. Bangarorin biyu sunyi takaddama ne kan ko suwaye ‘yan asalin jihar da kuma wadanda za su yi shugabanci. Kan haka ne wasu ke ganin bayan ga kabilanci na addini, rikicin Jos na da alaka da siyasa. An samu asarar rayuka da ma dukiyoyi masu dimbin yawa tun daga lokacin da aka fara zaman doya da manja a garin, wato daga shekara ta 2001 zuwa 2010. Rikice-rikicen da aka yi ta yi a Jos a shekarun baya kan bazu zuwa jahohin dake makwabtaka da ita kamar Gombe da Bauchi.
Ana cikin wannan yanayi ne kuma mu ka tsinci kanmu a halin da muke ciki har izuwa yau, wato rikicin Boko Haram, wanda ya auku a watan Yulin shekara ta 2009, inda wadansu matasa karkashin jagorancin Muhammad Yusuf dake adawa da ilimin Boko da aikin gwamnati suka kaddamar da yaki kan jami’an tsaro da ofisoshinsu a cikin birninmu na Maiduguri a jihar Barno.
Irin kashe-kashe da zub da jini da kuma tashe-tashen hankulan da tun farko ake ganinsu a yankin Arewa maso gabas inda ake fama da talauci, yanzu kuma ya bazu zuwa sassan Najeriya da wajenta.
Kungiyar Boko Haram tana iya fitowa fili tana kalubalantar gwamnatin Najeriya a yunkurinta na shimfida abin da a cewarta shi ne tsarin Shari’ar Musulunci. Abu ya yi abu. Boko Haram na kai hari ta ko ina, duk dai a kokarin cimma manufofinsu.
Kungiyar Boko Haram ta kashe dubban dubatan mutane, wanda kuma akasarinsu ‘yan Arewacin kasar ne, tun daga lokacin da aka fara rikici a 2009. Kungiyar Boko Haram ta fara kai hare-haren farko kan ofisoshin ‘yan sanda da na sauran jami’an tsaro. Hare-haren nakiya (Bom) na mota na farko ya wakana ne a hedikwatar ‘yan sanda dake Abuja da kuma ofishin Majalisar dinkin duniya dake babban birnin tarayya na Abuja. Kungiyar ta fadada wuraren da take kai ma hare-hare daga ofisoshin ‘yan sanda zalla, zuwa ga Masallatai da Majami’ai har ma da malaman da ba su yarda da akidarta su ba.
Tun bayan shekarar 2010, wannan zub da jini ya bazu ya tsallake iyakar Barno da ma Najeriya. Zub da jinin da kungiyar Boko Haram ke yi ya samu karin tallafi ko tagomashi, daga abubuwan da suka faru a kasar Mali daga 2011 zuwa 2012 inda ‘yan tawaye masu alaka da Al-Ka’ida suka kusan kwace kasar, kafin sojojin Faransa su ja musu burki a watan Janairun 2013.
Yau kimanin shekaru goma kenan mu na fama da tashe-tashen hankulan da zub da jini a dalilin kungiyar Boko Haram, sai ga jihar Zamfara ma ta dauka, kullum a cikin kashe-kashe da zub da jinin al’umma ake. Yau garkuwa da mutune ya zama ruwan dare a Arewancin Najeriya, kai kace babu gwamnati a kasar.
Abubuwan da ke faruwa a ’yan kwanakin nan tsakanin mabiya mazhaban Shi’a da gwamnatin Najeriya na sake barazana ga zaman lafiyar kasar, musamman ma ga Arewa.
A hakikanin gaskiya wannan kam gwamnatin Najeriya ce ke alhakin tada zaune tsaye a kasar, musamman idan mukayi duba da umarnin da kotu ta bayar na a saki shugaban mabiya mazhaban Shi’a.
Abin da mafi yawancinmu basu sani ba wasu kuma suka mance, shi ne, Mohammed Yusuf (shugaban kungiyar Boko Haram) wasu ‘yan tsirarin matasa ya mallaka a birnin Maiduguri, inda suka kaddamar da yaki kan jami’an tsaro da ofisoshinsu a cikin birnin, daga nan kuma kashe-kashe da zub da jini da tashe-tashen hankula suka zamo ruwan dare a yankin Arewa. A yayin da wannan tashe-tashen hankali ke bazuwa zuwa wasu sassan na Najeriya, har ma da makwabtanta, fargaba tana kara yawaita saboda gwamnatin Najeriya ta kasa tabuka komai.
Yau kimanin shekaru goma ke nan gwamnatin Najeriya ta kasa murkushe kungiyar Boko Haram, to yaya kuma kungiyar ‘yan uwa musulmi ta Shi’a, wanda a kusan dukkan kananan hukumomin kasar akwai su?
Idan almajiran Mohammed Yusuf da basu wuce a kidayasu ba an share shekaru goma gwamnatin Najeriya ta kasa murkushe su! To yaya kuma almajiran Zakzaky?
Innalilahi wa’inna ilahirraji’un!
Wai shin yaushe Arewa zata zauna lafiya ne? Wasu irin zunubai ‘yan Arewa suka aikata har Ubangiji ya jarrabe su da rashin zaman lafiya?
Zanso ‘yan uwana su amsa mini wadannan tambayoyin domin musan ta hanyar da zamubi wajen ceto Arewa daga wannan halin da ta tsinci kanta.
A karshe ina rokon Ubangiji Allah yasa Arewa ta zauna lafiya, kana kuma ya hada kawunan dukkan mabiya firkokin addinan kasar. Amin.
Daga dan ’yar uwanku, Mohammed Bala Garba, Maiduguri. 08098331260.