Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home NAZARI

Yaushe Za A Samar Da Riga-kafin Maleriya A Nijeriya?

by Muhammad
April 4, 2021
in NAZARI
4 min read
Maleriya
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Najeeb Maigatari,

A rubutun da ya gabata na dan kawo wasu kadan daga cikin dalilan da suka sanya samar da rigakafin cutar zazzabin cizon sauro ya na da wahala. Wannan karon kuma zan dora ne da amsar tambayar aboki na: da gaske ne ba a damu da samar da rigakafin Malaria ba?

 

Yunkuri na farko na samar da rigakafin cutar Malaria an fara shi ne a wajajen 1960 kuma har zuwa yau ana yi; musamman bayan ganin irin barnar da ta yi akan kwayoyin garkuwar jiki tun a lokacin yakin duniya na biyu. Wani rahoto na gidauniyar taskace tarihin sojojin Amurka ya bayyana cewa cutar Malaria ta kashe akalla sojojin Amurka 60,000 lokaci guda. Abun lura, tun kafin lokacin yakin duniya na biyu ana yin ta, har ma akwai maganin ta da aka samar.

 

Daya daga cikin hanya mafi inganci ta dakile cututtuka masu yaduwa shi ne samar da kariya ga al’umma (ta yanda za’a rage yawan masu kamuwa da kuma yada cutar), wannan ya sa cibiyoyin bincike da dama suka dukufa wajen samar da rigakafin zazzabin cizon sauro. Wasu daga ciki sai sun yi kamar za su yi nasara, daga baya kuma sai gwaji ya nuna akasin abun da ake fata, kamar misali a shekarun 1990s an yi ta gwajin wani rigakafin Malaria (SPf66) a guraren da ta barke, amma daga karshe ba a samu nasara ba.

 

Har zuwa yanzu, duk da akwai rigakafin cutar da ake ta kokarin samar wa daga cibiyoyi da dama, guda daya kacal ce aka samu nasarar gwajin tare da samar da sakamako mai inganci (duk da ita ma ba sosai yanda ake fata ba). Kuma yanzu haka ana amfani da ita a wasu kasashen yankin Afrika. Kasashen da ake amfani da ita su ne: Malawi, Ghana, da kuma Kenya.

 

Wani kamfanin hada magunguna GlaxoSmithKline (GSK) da ke kasar Ingila ne ya samar da rigakafin bayan aikin bincike da gwaje-gwaje na fiye da shekaru 30. Sannan kuma daga 2009 zuwa 2014 kuma aka samar da hadin gwiwa tsakanin fitattun wasu kungiyoyin samar da magunguna/rigakafi, kwamitin kwararru a hukumar lafiya ta duniya (WHO), gidauniyar Bill Gates da matar shi, tare da wasu cibiyoyin bincike na kasashen Afrika guda bakwai inda

aka tantance inganci, illa da kuma amfanin rigakafin wanda ya kwashe shekaru 5 ana yi.

 

Kasashen na Afrika guda bakwai su ne: Burkina Faso, Gabon, Ghana, Kenya, Malawi, Mozambikue, da Tanzania, wanda bayan an gama, sakamakon binciken ya nuna cewa: rigakafin ya

yi aiki kimanin kaso 39 cikin darri na yaran da suke fama da cutar (ba mai tsanani ba), sannan ya yi aiki kaso 29 cikin dari ga yaran da ke fama da cutar mai tsanani. Wato kenan, yara 4 cikin 10 a kashi na farko, da yara 3 cikin 10 a kashi na biyu.

 

Wannan babban kalubale ne, tunda ingancin rigakafin ba shi da yawa sosai. Amma kuma wani sakamakon binciken da kamfanin GSK ya gudanar a shekarar 2013 ya nuna rigakafin ya na rage yawan mutuwa ga yara kanana da kusan kaso

50 cikin dari ga jarirai tare da karin wani kaso 25 cikin dari. Amma duk da haka, sakamakon bai gamsar irin yadda ake bukata ba.

 

A hannu guda kuma, a shekarar 2018 akalla mutum 405, 000 ne su ka mutu ta sanadiyyar kamuwa da Malaria a duniya, kuma daga cikin wannan adadin, kimanin kaso 67 cikin dari yara ne ‘yan kasa da shekaru biyar a duniya, yayin da kaso 85 na wadanda su ka mutun, sun fito ne daga nahiyar Afrika, kana kuma

Nijeriya ita ce kan gaba da kaso 24 cikin dari na adadin wadanda cutar ta halaka a nahiyar.

 

Har wala yau, daga 2010 zuwa yanzu, cutar Malaria ta yi sanadiyyar rasuwar

miliyoyin mutane, wadanda mafi yawa kananan yara ne- musamman a nahiyar Afrika, wanda hakan ya sa yara yan kasa da shekara 5 su ka fi fuskantar barazanar hadarin rasa rayukan su daga cutar idan ta kama su.

 

Wanda bisa wannan dalili, duk da karancin ingancin rigakafin da kamfanin harhada magunguna na GSK ya samar, kwamitin kwararru da ke aikin lura da tantance ingancin magungunan rigakafi na hukumar lafiya ta duniya (WHO), cibiyar tabbatar da ingancin magani (FDA), da sauran cibiyoyin bincike na kasashen Afrika a 2019 suka kulla yarjejeniyar fara yin rigakafin ga yara kanana don ba su kariya daga illar cutar.

 

Haka kuma, kasashe da dama ne a nahiyar Afrika su ka yi burin shiga cikin tsarin inda za a fara yin rigakfin, amma guda uku ne kawai aka zaba daga ciki (Ghana, Malawi, da Kenya). Wanda kawowa yanzu, a wadannan kasashen su na da cibiyoyi na musamman da ke lura tare da sanya ido wajen gudanar da rigakafin, inda aka mayar da ita kamar

sauran rigakafi da ake gudanarwa.

 

Kuma daga cikin abubuwan da aka WHO ta yi la’akari da su wajen zaben wadannan kasashen don fara rigakafin maleriya su ne: bayyana ra’ayin ma’aikatar lafiya ta kowace kasa, ta hanyar nuna bukatar a saka ta ciki, tsarin yin rigakafi mai inganci a kasa, yawan adadin yaran da ke fama da cutar a yankin, da kuma mafi muhimmanci kwarewar kasa wajen iya tantance duk wani illar da rigakafin zai iya kawowa, kasar tana cikin inda aka yi gwajin farko, da sauran su.

 

Wanda zuwa yanzu za a ci gaba da yin wannan aikin har nan da 2023, kafin a gama tantance ko za a yi wa sauran

yankunan baki daya ko ya ya, sannan zuwa yanzu babu wani rahoton cewa an samu wata matsala daga rigakafin. Kuma kari akan haka, matakin ya taimaka wajen samun raguwar adadin masu fama da cutar a yankunan da aka gudanar da rigakafin, sannan ko aikin zai ci gaba, wanda lokaci ne kawai zai bayar da wannan amsa.

 

A karshe, dangane da amsar tambayar da abokina ya yi: wadannan bayanan sun tabbatar da cewa akwai rigakafin zazzabin Malaria, sai dai ba a fara amfanin da ita cikin kasashen duniya masu yawa ba kamar sauran rigakafin da ake yiwa yara ba, kuma kila hakan bai rasa nasaba da rashin inganci sosai, da kuma kokarin tantance illar ta. Kuma har

wala yau, akwai wadansu rigakafin da ake gwajin su har yanzu, wasu daga ciki suna nuna alamun nasara.

Karin bayani: A wannan rubutun ina yawan ambatar ‘inganci’ amma ko kusa

wannan ba ya na nufin rigakafin jabu ba ne ko kuma akwai guba a cikin shi da makamantan su ba. Ina nufin ‘efficacy’ ne: mutane nawa ya iya karewa daga kamuwa da cutar ake kokarin karewa

a matakin gwaji? Haka zalika, idan na ce ‘illa’ ina nufin ‘side effects’ ne, wanda kowane magani/rigakafi a duniya yana da shi.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Sanata Barkiya Ya Tallafa Wa ‘Yan Kasuwar Babbar Kasuwar Katsina Da Naira Naira Miliyan 20

Next Post

Tabarbarewar Tsaro: Me Yake Faruwa Da ‘Yan Nijeriya?

RelatedPosts

Tarbiyyar ‘Ya Mace A Zamanance

Tarbiyyar ‘Ya Mace A Zamanance

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Daga A'isha Muhammad A wanna Mukalar zan yi duba ne...

Lokaci

Muhimmiyar Tsaraba Ga Ma’auratan Jiya Da Na Yau

by Sulaiman Ibrahim
1 week ago
0

Daga Yusuf Kabir Aure yana daya daga cikin abin da...

Tsokaci A Kan ‘Telegram’ Da Yadda Ake Amfani Da Shi

Tsokaci A Kan ‘Telegram’ Da Yadda Ake Amfani Da Shi

by Muhammad
2 weeks ago
0

Daga Ibrahim Sabo, (ibsmait2020@gmail.com) 08032076472: Telegram tana daya daga cikin...

Next Post
Jami'an Tsaro

Tabarbarewar Tsaro: Me Yake Faruwa Da ‘Yan Nijeriya?

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version