Yaushe Za A Daina Zubar Da Jini A Nijeriya?

Akwai matukar tashin hankali yadda kullum ake  samun yawaitar asarar rayuka da dukiyoyin jama’a babu gaira babu dalili a kasar nan, musamman baya-bayan nan rikicin da ya barke a garin Ile-Ife na Jihar Osun da Zaki Biam na Jihar Binuwai. Wadannan kashe-kashe suna neman fito da maitar wasu ‘yan Nijeriya fili kan bukatarsu ta zukar jinainan ‘yan uwansu, wanda hakan ke jefa ayar tambaya kan imaninmu da dan’adamtarmu. Lamarin har ya kai munzalin da shi kansa Shugaba Muhammadu Buhari abun ya daure masa kai, yana kokwanto anya ‘yan Nijeriya sun san darajar dan’adam kuwa.

Tsakanin ‘yan shekarun da suka gabata, babu wata rana da ta wuce ba tare da bullar rahoton an kashe wani ko wata ba, kisa wanda ya wuce hankali. Hanyoyin da wadannan mugaye ke bi wajen aikata ta’asa abin tsoro ne matuka, ba su da imani daidai da cikin cokali. Sun mayar da ‘yan uwansu tamkar dabobi, a wasu lokutan ma dabba ta fi ‘yan uwansu daraja; a wurinsu, yin gunduwa-gunduwa da gangar jikin makwabtansu ba wani abu ba ne; su kashe; su bizne, su daddatsa; su watsar kan tituna sannan kuma rika murnar irin barnar da suka yi a bayyane. Shin yaushe za a daina zubar da jinin ‘yan Nijeriya ne?

Wadannan kashe-kashe sun dauki sabon salo tun bayan dawowar tsarin mulkin dimukradiyya sakamakon tsagerun matasa da ‘yan siyasa ke amfani da su a matsayin masu kare tawagarsu daga harin ‘yan adawa. Suna ba su mamaki da miyagun kwayoyi su yi abin da suka ga dama har zuwa lokacin zabe. Inda gizo yake sakar shi ne, bayan zabe sai a bar su da makamai a hannu ba tare da an karbe ba, su kuma tun da ba saiti ke garesu ba, kan wata biyan bukatarsu kansu, sai su zama jagororin kansu, ba kwaba balle fada. Da yawan mutane sun tafi a kan wannan shi ne jijiyar da ta yi sanadin bullar bishiyar da ta yi ganyen ta haifar da ‘ya’yan kungiyar Boko Haram, wadanda cikin kankanin lokaci suka addabi Nijeriya da duniya baki daya.

Sojoji na tsaka da fatattakar wadancan masu tayar da kayar bayan, sai kuma ga shi wasu na’ukan makasan sun sake bulla da sunaye kala-kala; ‘Yan Bindiga ko kuma Fulani Makiyaya, inda suke neman ture wadancan su kafa nasu sansanin shan jinin jama’a. Suna kai farmaki, su kashe na kashewa su raunata na raunatawa, idan hali ya yi kuma su sace mata da tsaffi. Baya ga wannan, ga rikicin kabilanci da yake shirin samun gindin zama, har yanzu kuma ba a dauko hanyar dakile shi ba.

Har yanzu kasar ba ta fita daga radadi sakamakon artabun sojoji da wata kungiyar addini a Kaduba ba, har ila yau, ga rikcin Kudancin Kaduna, rikicin kabilar Agatu a Binuwai, Nsukka a Inugu, Zaki Biam a Binuwai sai Ile-Ife a Osun, dukkan wadannan rikice-rikice masu matukar muni suna yawo a kwakwalenmu, kasancewar sun zamo sanadin asarar rayuka da dimbin dukiya.

A duk wadannan artabun da ake yi, ba dai-daikun mutane ne ke mutuwa ba, a’a, daruruwa ne ko a ce dubbai kuma ba yaki ake yi da wata kasa ba, balle a ce. Jami’an tsaro sun bayyana masu aikata wadannan laifuka a matsayin ‘bata-gari’ wadanda suke son tada zaune tsaye, amma babu koda mutum guda da aka kama balle a gurfanar da shi gaba kuliya.

Mun ga dacewar fito da abubuwa fili, cewar Gwamnoni Jihohi suna karbar kaso mai tsoka daga Gwamnatin Tarayya da sunan Tsaro. Akwai rundunonin ‘Yan Sanda, Jami’an Tsaro, Sansanin Soji da sauran jami’ai masu damara. Amma duk wadanda sun gaza dakile kashe-kashen da ke ci gaba da yawaita a cikin al’umma tamkar sun mance da hakkinsu na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa bisa alkawari da suka yi.

Kafin yanzu, mafi yawacin zarge-zargen da jami’an tsaro ke yi shi ne cewar, masu kai farmakin ba ‘yan Nijeriya ba ne, suna sulalowa ta iyakokin kasa, su yi barna sannan su fice. Idan har ta tabbata haka ne baki na kawo wa ‘yan kasa hari, to lallai ana bukatar mutumin da zai jagorancin yaki da wannan rashin hankalin.

Mun fahimci ‘yan Nijeriya da yawa suna da ra’ayin cewa jami’an tsaro sun gaza matuka wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, wanda hakan a kullum yake kara zubarwa da kasar mutunci a idon duniya. Kasashen Duniya, ciki har da Majalisar Dinkin Duniya suna kokawa matuka kan kashe-kashen babu gaira babu dalili a Nijeriya.

Shugaba Kasa ya yi wata ganawa ta musamman da Shugabannin Tsaro kwanakin baya don su yi masa bayanin matakan da suke dauka wajen shawo kan wadannan rikice-rikice. Fatanmu shi ne, hukumomi su yi mai yiwuwa don tabbatar da ganin an dawo da martabar ran dan’adam. Halin da ake ciki a yanzu na rashin yarda da aminci tsakanin kabilu, lallai ya dace gwamnati ta yi wani abu, domin zaman lafiya ya fi zama dan sarki!

 

Exit mobile version