Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
ADVERTISEMENT
Home Hannunka Mai Sanda

Yawaitar Hadurra: Gajiya Da Raunin Tunanin Direba

by Muhammad
February 19, 2021
in Hannunka Mai Sanda
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Sauran cikon ababe biyun (2) da masana suka ayyana, a matsayin wadanda ke taimakawa wajen afkar da haduran ababen hawa cikin wannan Kasa, ga su kamar haka;

6- Gajiyar Direba, da kuma

7- Raunin Tunanin Direba

Su ma wadannan ababe biyun da aka ambata, a gurguje, za mu dan fasa su, tamkar irin yadda muka yi wa takwarorinsu (sauran ababen da ke haddasa haduran) a baya, sai kuma mu karkare wannan rubutu da gabatar da mafita, da wadancan masana da sauran manazarta ke ganin, za su taimaka zuwa ga, takaice, gami da rage adadin wadannan hadura da ake samu dare da rana bisa titunan wannan Kasa tsawon lokacin da, har kawo yin wannan rubutu, bangaren gwamnati da na al’umar gari, sun gaza nuna wani hobbasa, ko karsashi na zahiri, wanda zai hakkake an tasamma magance wannan mummunar annoba ta rasa rayukan al’umar Kasa, wanda a akasarin lokuta, wadanda ba su ji ba, ba su gani ba ne ke tagayyara. Da yawan lokuta, wadanda ke taka rawa ta sama da kashi 80% na afkuwar haduran, kan tsallake rijiya da baya ne, su bar “yan-ba-ruwanmu cikin rintsi!.

6- Gajiyar Direba

Misali, ga direba, an yi masa lodin kaya daga Kano, za shi Lagos. Bayan ya je Lagus din, washegari kuma, sai a ka yi masa wani lodin kayan daga can, zuwa garin Maiduguri. Bai yi ko da hutun kwanaki biyu a can Ikkon ba, da sunan ya huta ya sarara, amma kuma don karfin-hali da rashin mafadi kuma, ya tasamma zuwa jihar Borno washegari.

Direbobin manyan motoci da ke jigilar kayayyaki daga wannan jiha zuwa waccan, za su fi fahimtar abinda marubucin ke nufi da gajiyar direba. Hatta maizuwa Kano daga Zariya jigilar sayo gurasa, muddin ya zamana yai zarya har sau uku a rana, daga Zariyan zuwa Kano, kuma ya kasance gari na wayewa, ya sake sako hancin motarsa zuwa Kano da sunan cigaban jigilar fataucin gurasa, ba tare da ya samu ya warware gajiyar jiya ba, zai zama akwai ayar-tambaya (?) a kansa na reto.

Ko da misalin da a ka gabatar dake kokarin nuna halin ko-in-kula da direbobi ke nunawa, na rashin samun isasshen bacci ko hutu, mutum bai fahimta ba, amma dai ya kan ji cewa, an tafka hadarin mota da mota, ko mota ta tintsira rami, ko ta tunkuyi wata bishiya, sakamakon barci da ya shammaci direban.

Na’am, direbobi iri-iri ne, haka ma wani kwazo ko juriya da da suke da shi, ya banbanta, saboda haka, ba za a yi saurin cewa, idan direba ya yi tuki zuwa lokaci kaza, to dole ne ya kwanta ya yi barci isasshe gami da huce gajiyar tafiya ba. Sai dai, duk cikar direbobin, duk kwarewarsu, wani abu ne sananne cewa, suna gajiya, sukan bukaci hutu, kuma ma sukan bukaci yin barci, amma sai su ki (ba dukansu ne ba).

7- Raunin Tunanin Direba

Abinda ake nufi da raunin tunanin direna a nan shi ne, mutum ne za ka samu gashi yana yin tukin wani abin hawa, amma saboda tsabar rashin sanin ka’ida da dokokin hanya, sai ya nemi afkar da hadari, ko ma ya afkar, amma kuma a lokaci guda, sai a ga yana neman yin kumfar-bakin wai shi ke da gaskiya. Idan ya zamana mushen tunanin wanda bai san ka’idar tuki ba ya cigaba da tafiya a haka, yanayin zai rika taimakawa zuwa ga samuwar taho-mu-gama na ababen hawa bisa titunanmu.

Babu shakka akwai abubuwa da dama, wadanda suke muddin za a dabbaka su, la-budda, za su matukar taimaka, zuwa ga rage adadi mai tarin yawa, na haduran da ke samuwa a bisa manya da kananan titunan wannan Kasa. Sanin kowane cewa, irin wadannan hadura, kan jaza afkuwar duk wani abin-ki ga Dan’adam. Zai iya rasa ransa kacokan. Wata gaba a jikinsa, na iya salwantar da ya rabu da ita ke nan har abada. Ya kan sami mummunar karaya da karama. Hankalinsa kan gushe har abada, sakamakon gamewar kwakwalwa da jini. Mutum kan susuce ya zamto wani dolo, sakamakon buguwa da ya hadu da, yayin hadarin. Akwai kananan raunuka da sauran ababen-ki, wadanda mutum kan hadu da, a duk sa’adda aka yi wata arangama da sunan hadari. Ga wasu daga mafita ko waraka game da yawaitar afkuwar haduran;

A- Ilmantar Da Al’uma

Ilmantar da al’uma dare da rana, game da sanin hakikanin dokoki da ka’idojin hanya, zai taimaka ainun wajen takaita haduran.

SendShareTweetShare
Previous Post

Kasashe 15 Da Maza Ke Wahalar Samun Aure Saboda Karancin Mata

Next Post

Bai’atur Ridwan: Sahabban Da Suka Yi Mubaya’a Da Manzon Allah Sun Yi Da Allah Ne (II)

RelatedPosts

Labarai Cikin Hotuna

Hannunka Mai Sanda Ga ‘Yan Takarar Gwamna A Jihar Kano

by Muhammad
1 week ago
0

alimailafiyasunusi@gmail.com - 08036064695. Satin daya gabata na yi fashin baki...

Gwagwarmaya

Tsokacin Kolawale (II) Yadda Ta Kaya Tsakaninsa Da ‘Yar Gwagwarmaya

by Muhammad
3 weeks ago
0

A makon da ya gabata, mun tsaya ne a inda...

Nijeriya, Ina Mu Ka Dosa?

Nijeriya, Ina Mu Ka Dosa?

by Sulaiman Ibrahim
1 month ago
0

Kalmar Nijeriya ina muka dosa, na nunawa mai karatu ne...

Next Post
Sahabban

Bai’atur Ridwan: Sahabban Da Suka Yi Mubaya’a Da Manzon Allah Sun Yi Da Allah Ne (II)

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version