Ba ya ga tafka gudu bisa hanya a matsayin guda cikin ababen da ke haddasa hadura bisa tituna musamman a irin Kasashenmu na Afurka, masu sharhi sun cigaba da gabatar da wasu sabubban ne kamar haka:
2- Yanayin Tabarbarewar Hanyoyi
Wani babban abin takaici cikin wannan Kasa shi ne, kamar yadda har yanzu masu tsayawa takarar kujerun-iko ke yin alkawarin samar da ruwan sha; wutar lantarki da sauransu, haka ma abin yake ta fuskar yin alkawuran samar da kyawawan hanyoyi domin ababen hawa.
Ko mai karatu ya san adadin lalatattun hanyoyin dake yin kilishi da rayukan “yan Najeriya a kullum?. Ga munanan ramuka tattare da hanyoyin, ga yin aikin kwangilar hanyoyin marasa inganci! An yi sabuwar hanya wannan Shekara, amma da mutum zai dawo bayan Shekaru uku, zai sha mamakin irin kazgaron da zai iske birjik bisa hanyar, sai dai idan a babban birnin tarayya na Kasa ne a ka yi ta, a nan, sai ta yi tsawon Shekaru lafiya sumul. Ashe bayan harkar ilmi da ta tsaro a wannan Kasa, akwai wani aiki da ya fi gyaran hanyoyinmu muhimmanci?. Na’am, mai karatu zai ji wannan tambayar wani banbarakwai, amsa ita ce, kare rayukan jama’ar Kasa, ya fi kowane irin aiki muhimmanci. Sai da rai ne, mutum zai mori duk wani abu na kyautatawa da za a yi masa a rayuwa, sai aka wayigarin cewa, ga wani abu da ke hadiye rayukan jama’a a kullum, amma gwamnatoci sun yi burus, sun ki daukar matakin kawo karshen wannan barazana, me hakan ke nusarwa?.
Ko masu mulki sun san cewa, suma suna taimakawa wajen wanzuwar ta’adar fashi da makami a Kasa, ta hanyar kin gyara titunana?. Ta tabbata, a duk sa’adda hanya ta yi muguwar lalacewa a dokar daji, ta yadda dole ne ababen hawa sai sun tafi sannu-sannu, kafin samun damar wucewa, a irin wannan yanayi, barayi kan fito daga maboyarsu ne su zalunci mutane. To, wake da alhakin gyara hanyar amma ya ki? Amsa gwamnati. Ta wannan sakaci ne gwamnatoci ke dafawa “yan fashi da makami a Najeriya.
Hanyar da ya dace a kammala gina ta cikin Shekara guda, amma sai a yi Shekara uku zuwa biyar ba a kammala ta ba. Misali, akwai wani titi a Kano, cikin karamar hukumar Dala, wanda ya tashi daga mahadar titin Goron Dutse zuwa unguwar Jakara, wanda ake tunanin tsayinsa bai wuce kilomita 5 ba, amma an fi Shekara 7 ba a kammala aikin titin ba. Ko mai karatu ya san adadin wadanda suka karye baras, a sanadiyyar lalacewa da rashin kammala aikin wannan titi na Goron Dutse zuwa Jakara?.
Adadin mutane nawa ne yanayin lafiyarsu ya tabarbare a sanadiyyar rashin kyawon hanyar (ta Jakara–G/Dutse), da kuma sakacin rashin kammala ta bisa lokaci? Ashe mai karatu bai san masu cutar Asima (Asthma), kurar titin, na ragargaje lafiyar jikunansu ba? Ko an fada maka cewa masu cutar tari, kura ba ta kara musu ukubar ciwo? Duk da cewa, wannan marubuci bai zurfafa bincike ba game da mugun alkaba’in da rashin kammala wannan titi ya jazawa al’umomin da ke rayuwa bisa titin ba, hada da wadanda ke zuwa wucewa, da sai ma a ce babu mamaki mugun yanayin titin ya ci ran mutum ko da guda ne, ko ma fiye!.
Wani abin mamaki da kuma Allah-wadai shi ne, ko mai karatu ya sani cewa, titunan da gwamnatocin Soji suka dankara cikin wannan Kasa, ko na farar hula albarka? To ke nan, menene amfanin Dimukradiyyar ga talakan Najeriya? Eh mana! An ce a karkashin inuwar Dimukradiyyar, ka fi “yancin magana ko a ce babatu, kuma kana ma da damar titse mai mulki, uwa-uba, za ma ka iya tuntsiro da shi daga kan kujerar mulki, sabanin lokacin mulkin Soja, to amma kuma sai gashi, titunan da ke cin rayukan “yan’uwanka da na sauran jama’ar Kasa, an fi kula da samar da su, da kuma gyara su a Mulkin Soja, ke nan, menene ranar mulkin Dimukradiyyar a gare ka?.
Kwatanta adadi da kuma ingantattun titunan da aka samar a lokacin mulkin Babangida da na Abacha, da kuma titinan da aka samar lokacin mulkin Obasanjo da na Goodluck da kuma na Buhari. Titinan wane lokaci ne suka fi yawa da kuma inganci? Wace iriyar Dimukradiyya ce ake cikinta a yau, wadda ba ta damu da salwantar rayukan “yan Kasa ba? In an bi ta 6arawo… Suma “yan Kasar, ba su dami da rayukan nasu ba. Sau nawa ne masu goyon bayan Honarabul Dan-dila da masu goyon bayan Honarabul Kumurci da Kerkeci, za a ga sun yi kwana da kwanaki a kafofin sadarwa na Fesbuk (Facebook) kowa na kare nasa naman-dajin, to amma ko mai karatu zai iya tuna wata rana guda, da masu banbancin ra’ayin addini ko na siyasa suka hade kawunansu wuriguda a waccan kafa ta sadarwa, suna masu hantarar Ciyaman, ko Gwamna, ko Shugaban Kasa, game da mugun tabarbarewar titunan Kasarmu? Ko an fada maka cewa, miyagun hadura da ake haduwa da su bisa tituna, na tantance dan akidar addini iri-kaza, koko dan akidar siyasa iri-kaza? Ashe lokaci bai yi ba, da Matasan dake yin gumurzu a tsakaninsu dare da rana, saboda banbancin Siyasa ko na Addini, na su yi kokarin samar da wani Dandamalin da za su rika yin magana da yawu guda ba? Ko mai karatu ya san masu mulki ba sa son a rika bai wa Matasa irin wannan shawara? Ta yaya ne za ku ci nasara haka a rarrabe?. Ko don saboda manyan Kasa sun fi yin mu’amula da jiragen sama ne, shi yasa ba su damu da gyara titunan Kasa ba, tamkar yadda suka damu da shawo-kan cutar Cobid-19?.