Yawaitar Shaye-Shaye Miyagun Kwayoyi Ga Matasanmu!

Tuni rahotannin dake kunshe da hannunka-mai-sanda suka mamaye ko’ina a kasar nan, bisa ga yawaitar shaye-shayen miyagun kwayoyi da sauran miyagun ababe masu illa da kuma lahanta kwakwalwa musamman ga matasanmu na Nijeriya.

Akwai kalubale masu tarin yawa ga Hukumar Hana Sha da Safarar Miyagun Kwayoyi ta Nijeriya, “National Drug Law Emforcement Agency” (NDLEA) wacce abin ya fi shafa kai tsaye. Hakika hukumar tana sane da rahotannin dake yawo game da karuwar shaye-shayen miyagun kwayoyin gurbata rayuwa da kuma hodar koken, wadda kuma a kullum kamawa da gurfanarwar da hukumar ke yi ya gaza kawo karshen wannan mummunar dabi’a dake ci gaba da faruwa tamkar wutar daji!

A cewar hukumar, yanayin da ake cikin ba kawai hannunka-mai-sanda lamarin ke bukata ba, illa a samu gudumawar dukkan bangororin da suka akamata wajen fuskantar wannan kaidi da aka kitsa mana wanda yake taka rawar gaske wajen canza illahirin alkiblar kasar da kuma fuskantar barazana mai yawan gaske anan gaba.

Da alama wannan lamari na ci gaba da gajiyar da kwararru akan fannin, musamman yadda lamarin ke cin karo da kokarin da suke ta hanyar yawaitar matasan dake bijirewa kamar yadda rahotanni ke yin nuni da hakan a kullu yomin. Lamarin mayen har ya kai ga matasa na shakar warin kwata, kashin kadangare da sauran dangogin kazanta daban-daban don neman yin mayen ta kowane hali. Sannan baya ga illar da hakan ke haifarwa ga yanayin lafiyarsu da kwakwalwarsu, yana kuma rawa wajen haddasa ayyukan assha da tsageranci kala-kala.

Haka zalika rahotannin kwararru sun tabbatar cewa mafi yawan ayyukan assha, ta’addanci da barna suna faruwa ne sakamakon shaye-shayen miyagun kwayoyin, haka nan kuma a duk lokacin da aka kama masu laifi, to akan samu tulin ire-iren wadannan miyagun kwayoyi a tare da su ko a gidajensu da sauran su.

Bugu da kari wani abu mafi hadari kuma shi ne yadda a kullum hodar koken ke kara zama mafi saukin samu ga matasan namu tamkar hantsi mai leka gidan kowa. Amma a gabanin wannan lokacin samun hodar koken abu ne mai wahalar gaske hatta a tsakanin mawadata da ma su mulki. Amma ban yanzu!

Ada can ana danganta ayyukan assha ga turawa ne kawai wadanda ake kallon a fina-finai, amma a yau bakaken fata sune kan gaba wajen aikata wadannan miyagun dabi’u. hasali ma dai ana danganta dukkan laifuka ga shaye-shayen miyagun kwayoyin har ma da ayyukan kungiyoyin asiri da tsafe-tsafe a tsakanin al’umma a yau.

Kuma fa mafi yawan wadannan matasa wasu ne ke daukar nauyin shaye-shayen nasu, musamman ‘yan siyasarmu na yau, don cimma munanan manufofinsu na siyasa kawai. Suna narka kudi ko nawa ne don tabbatar da cewa matasan sun ci gaba da zama cikin maye don amsa kiransu a koda yaushe.

Wannan kuma a fili yake cewa daidaikun attajirai da wasu ‘yan siyasa ke haddasa gagarumar cikas tare da haifar da koma bayan da ake samu wajen yaka ko murkushe wadannan dabi’u wadda ga alama yana neman gagarar ita kanta hukumar NDLEA ta Nijeriya. Wannan kuma hakika babban abin dubawa ne.

A mahangarmu, akwai matakai da daman gaske da Nijeriya za ta iya dauka wajen taimakawa wadannan matasa daina ko yin ta’ammali da miyagun kwayoyin, sannan ta tserar da su daga gabar halakar da suke kanta a yanzu. Farko dai iyaye sai sun shigo cikin lamarin, sun tsaya sosai wajen nuna wa ‘ya’yansu irin hadarin dake tattare da wannan dabi’a. Haka zalika makarantu na da rawar takawa a wannan bangaren wajen kirkirar cibiyoyin tarbiyya a makarantunsu, don aza dalibai bisa turba nagari tare da kwadaitar da su kyawawan dabi’u wadanda za su kai su ga zama abin koyi a tsakanin al’umma.

Haka nan kuma, illolin dake tattare da shaye-shayen na matukar gurbata yanayin al’adunmu da mutuncinmu na asali da aka sanmu akan su tun ma kafin zuwan bature. Sannan bugu da kari iyaye, makarantu, malaman addinai, cibiyoyin addinai da kuma dukkan matakan gwamnati da hukumominta su kara azama wajen tunkarar wannan babban kalubale don sake fuskantar da matasanmu zuwa ga hanya madaidaiciya.

Sannan har ila yau akwai karancin kokari ga hukumomi wajen dakile cikayyar kayan shaye-shaye a kasuwanninmu da sauran wurare. Idan har ana son magance wannan da’ata, to wajibi ne a aiwatar da dokar ta baci a bangaren safarar su zuwa cikin kasar nan.

Domin fa babu kasar da zata yi wasa ko sakaci da makomarta, ko ta sadaukar da matasanta ga halaka, muddin kuwa haka ta faru, to kasa ta yi asarar makomarta wadda kuma ko shakka babu cewa matasan nata ne zasu karbi ragamar jagorancinta bisa halayya nagari ko kuwa akasin hakan.

Exit mobile version