Yawan Ba-ni-ba-ni Na Haifar Da Gori ga ‘Ya Mace – Zahra BB

Zahra BB

A yau wannan makon shafin nan ya samu karbar Fatima Bello Bala da aka sani da (Zahra BB), inda ta tattauna da wakiliyarmu Zulaihat Haruna. Ta bayyana wa masu karatu cewa, yawan ba-ni-ba-ni, ya kan haifar da gori, don haka a cewarta dogaro da kai ya fi komai dadi da zama cikin kwanciyar hankali, kamar dai yadda za ku karanta.

Da fari za mu so sanin cikakken sunanki da tarihinki?

Sunana Fatima Bello Bala (Zahra BB). Ni haifaffiyar Jihar Sakkwato ce, a Karamar Hukumar Sokoto ta Arewa. Na yi karatun boko da na addini duk a nan Sokoto.

 

Shin Fatima matar aure ce?

A’a ba ni da aure.

 

Malama Fatima ‘yar kasuwa ce ko kuwa ma’aikaciya ce?

Ni ‘yar kasuwa ce, aikin ma muna sa ran samu In sha Allah.

 

Wanne irin kasuwanci kike yi?

Ina sarrafa Madara ta zama kayan makulashe

 

Shin me kasuwancin naki ya kunsa? Ma’ana kamar me da me kike sarrafawa?

Ina sarrafa madara ta zama Alewar madara/Tuwon madara haka zalika ta koma Gullisuwa da dai sauran su.

Me ya ja hankalinki har kika shiga wannan kasuwancin?

Abin da ya ja ra’ayina bai fi son dogaro da kaina ba, kasancewar dogaro da kai shi ne abu mafi muhimmanci a rayuwar matasa. Wanda zai sa ka tsaya da kafafuwanka ba tare da abin wani ya tsone maka ido ba. Yawan bani bani, ya kan haifar da gori ko wulakanci a wajen duk wanda kake yawan roko, shi ya sa ma masu hikimar zance ke cewa, da a baka kifi kullum gwanda a nuna maka yadda ake kama kifin. Rashin dogaro da kai yana daga cikin abin da ke jefa matasanmu a cikin wani hali marar kyau daga cikinsu har da fadawa shaye-shaye. Idan kana da sana’arka to baka da wani lokacin batawa a banza,  wanda a cikin sana’ar sai ka ga ka amfanar da kanka har da waninka.

 

Fatima ba ki fada mana matakin karatu ba?

 

Na kammala diploma, kuma yanzu na samu gurbin karatu a Jami’ar Sakkwato. Inda na shiga da ‘Direct Entry’.

Wanne irin kalubale kika taba fuskanta a cikin sana’arki?

Ita rayuwa ba za a ce babu kalubale a cikinta ba. Amma daya daga cikin abin da muke fuskanta bai fi kwastomominmu da wasu lokutan su kan kasa fahimtar yanayi ba. Idan na ce yanayi ina nufin tsadar kayan da muke ciki, kowa dai yana yin Sallah don lada, amma idan aka sanar masu farashin kaza ya karu sai su rika ganin kamar tsada ce kake yi masu. Wasu kuma sai kun gama ciniki sun saka maka rai da sayen sana’arka sai ka ji su dif kamar an aiki bawa garinsu.

Zuwa yanzu wadanne irin nasarori kika cimma?

Nasarori kam mun same su, kuma muna kan samun su. Saboda duk inda ka samu rufen asirin ka yi hidimar kanka har ma da ta wasu, iya nasara an same ta, bugu da kari kuma ga sanayyar mutane duk inda sunan ka ya gilma an san shi ko da baka taba taka wajen ba, hakan ma duk nasara ce.

 

A da can da kike karama mene ne burinki?

To burika da yawa, amma babban burina bai fi na ga na zama mai dogaro da kaina ba.

 

Wanne abu ne ya fi faranta maki rai game da sana’arki?

Babu abin da nafi jin dadinsa irin idan ka yi maganar kana so ka saya kai tsaye ka biya kudi.

 

Ta wacce hanya kike bi wajen tallata sana’arki?

Ta Soshil Midiya, kafofin sada zumunta na kan tallata.

 

Dame kike so mutane su riƙa tunawa dake?

Ina son idan mutane suka tuna ni su yi farin ciki, su tuna kyakkyawar alakar da muka yi da su cikin aminci.

 

Ga karatu, ga kuma hidimomin sana’a, shin ta yaya kike samun damar gudanar da hutunki?

A rayuwa komai yana son tsari, na kan tsara komai nawa ta yadda zai zo min da sauki, na kan ware lokutan aiwatar da komai nawa, daga cikin kowa har da hutuna.

Zahra BB

Wanne irin addu’a ne idan aka yi maki kike jin daɗi?

Allah ya yi miki albarka tare da sauran addu’o’in fatan alkhairi, ina jin dadin a yi min su sosai.

 

Wanne irin goyon baya kike samu daga wajen Iyaye da ‘yan’uwanki?

Ina samun goyon baya sosai daga wajen su tare da yi min fatan alkhairi a ko da yaushe.

 

Kawaye fa?

Kawaye na ma a kullum suna bi na da addu’a, ba ni da bakin gode masu, sai dai ina yi masu fatan Alheri kuma ina rokon Allah ya bar mana amincinmu har abada.

 

Me kika fi so cikin kayan sawa, da kayan kwalliya?

Ina son riga da siket sai doguwar riga. To gaskiya ban fiye yin kwalliya ba.

 

A ƙarshe wanne irin shawara za ki ba ‘yan’uwanki mata?

Shawarar da zan bawa ‘yan’uwana mata ita ce,  su dage sosai wajen neman na kan su. Su tsayu a kan dugadugansu. Ko da kina da aure za ki taimaka wa ‘ya’yanki da mijinki, idan baki da shi za ki ragewa iyayenki wani nauyin. Kin huta ta zama ‘yar bani-bani, tun ana baki cikin dadin rai har a zo wani lokacin za a rika hade miki fuska.

 

Exit mobile version