“Yawan Fararen Hular Da Suka Hallaka A Siriya Da Iraki Ya Karu A 2017”

Wata kungiya mai zaman kanta da ke sa ido kan yakin da Amurka ke jagoranta da mayakan IS a kasashen Siriya da Iraki, ta ce yawan fararen hular da rayukansu ke salwanta a dalilin yakin ya karu da kashi 200 a shekarar 2017.

Kungiyar mai suna Airwars, ta ce alkaluman rayukan fararen hular da suka salwanta, ya zarta na shekarar 2016, inda aka hallaka fararen hula tsakanin 3,923 da kuma dubu 6,102 a kasashen na Iraki da Siriya.

Kungiyar ta daganta karuwar rasa rayukan da yadda a shekarar da ta wuce, mayakan IS suka ja tunga a garuruwa ko birane masu yawan jama’a, musamman a birnin Mosul na Iraki da kuma Rakka da ke kasar Siriya.

Exit mobile version