Kamfanin layin dogo na kasar Sin ya bayyana yau Lahadi cewa, an yi jigilar kayayyaki tan miliyan 970 ta hanyar sufurin layin dogo na kasar Sin a cikin watanni ukun farko na shekarar 2025, adadin da ya karu da kashi 3.1 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara. Kana, Yawan kayayyakin da aka yi dakon su a kowace rana ya kai tarago 179,000, karuwar kashi 4.2 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.
Kazalika, sufurin layin dogo ta saukaka yin kasuwanci tsakanin kasa da kasa a wannan lokacin. Musamman ma, jiragen kasan dakon kaya tsakanin kasar Sin da tsakiyar Asiya sun yi jigilar kayayyaki sau 3,582, wanda ya nuna karuwar kashi 25.5 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, a cewar kamfanin layin dogon. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)