Aminu Mukhtar Dan-Alhaji" />

Yawan Karbo Bashin Da Gwamnati Ke Yi Bai Da Amfani Ga Kasar Nan -Farfesa Dadari

Farfesa Dadari

Wani Malami a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, Farfesa Salihu Adamu Dadari ya koka a bisa yadda gwamnatin tarayya ke yawan karbo bashin kudade daga hukumomin da ke bayar da lamuni na kasashen duniya.

Malamin wanda ya bayyana haka a zantawarsa da wakilinmu a garin Saminaka, ya lura tare da nuna damuwarsa cewa galibin lokuta wadansu jami’an gwamnati marasa kishin kasa kan wawure kudaden bayan an karbo bashin.Don haka ne ya ce karbo bashin da gwamnatin tarayyar ke yi bai da wani amfani ga jama’ar kasa.Ya yi bayanin cewa kafin hukumomin bayar da lamunin su bayar da bashin ga kasar nan sai sun gindaya tsauraran sharuda da ka’idoji da sau da yawa kan yi illa ga tattalin arzikin kasa.

Farfesa Salihu Dadari ya kawo shawarar cewa a maimakon ci yo bashin, kamata ya yi gwamnatin ta lalubo hanyoyin toshe kafofin da kudadenta ke silalewa, tare da daukar matakan rage tsadar gudanar da harkokin gwamnati.Ya ce cin hanci da rashawa su ne manyan matsalolin da ke targade ci gaban kasar nan da kuma hana ta sakat.

Da ya juya ga batun tsaro kuwa, Malamin jami’ar ya bukaci shugaba Muhammad Buhari ya sallami shugabannin rundunonin tsaron domin kuwa sun gaza kai wa bantensu.Acewarsa, idan aka bai wa mutum mukami kuma ya gaza, ya kamata a sauke shi a kawo wanda ake tunanin zai yi abin da ya dace.Ya nunar da cewa ko harkar tsaron ma tana kara tabarbarewa ne saboda cin hanci da rashawa da suka mata katutu.

Ya zargin cewa an yi ta fitar da kudade domin a sayo makamai don amfanin sojojin da ke fagen fama amma an ki sayo makaman wanda hakan ya sa sojojin suka kasa katabus.Ya ce rashawa ce babbar matsalar da ke hana ruwa gudu a dukkan fannonin ci gaban kasar nan.Daga nan sai ya yi tambihi ga jama’ar Najeriya su kasance masu kishi da son ci gaban kasa tare da gyara halayensu ta yadda za a sami ci gaban da ake bukata.

Exit mobile version