Yawan Kayayyakin Da Sin Ta Samar Ya Wuce Misali Ko Damuwar Amurka Ta Wuce Kima?
  • English
  • Business News
Thursday, October 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yawan Kayayyakin Da Sin Ta Samar Ya Wuce Misali Ko Damuwar Amurka Ta Wuce Kima?

byCGTN Hausa
1 year ago
Sin

Ran 24 ga wata, sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya fara ziyarar aiki a kasar Sin, karo na biyu a wa’adin aikinsa. Bisa labarin da kafofin yada labarai na Amurka suka bayar, an ce, Blinken zai ci gaba da shafawa kasar Sin bakin fenti kamar yadda sakatariyar baitul malin kasar Janet L. Yellen ta yi, kan wasu bangarorin da Sin take da fifiko sama da Amurka, da cewa wai “Yawan kayayyakin da masana’antun Sin ke samarwa ya wuce kima”. Amma ko da gaske ne yawan kayayyakin da Sin ta samar ya wuce misali, ko yawan damuwar Amurka ya wuce kima?

Bari mu duba wasu alkaluma. Hukumar kula da makamashi ta duniya wato IEA ta yi kiyasin cewa, domin cimma burin samun daidaito tsakanin yawan hayaki mai dumama yanayi da za a fitar da yawan abubuwan da za su shawo kan hayakin, zuwa shekara ta 2030, za a bukaci motoci masu amfani da makamashi mai tsabta kimanin miliyan 45, yayin da za a bukaci wutar lantarkin da yawansa ya kai gigawatt 820 daga sabbin injunan samar da wutar lantarki masu amfani da hasken rana. Wadannan alkaluma sun ninka sau 4.5 da 4 bisa na shekarar 2022. A matsayin kasa mafi karfi a fannin samarwa da sayar da motoci masu amfani da makamashi mai tsabta, kasar Sin ta samar da motocin da yawansu ya kai fiye da miliyan 9.5 a bara, kuma ta fitar da kimanin miliyan 1.2 ketare. Wato adadin da ya kai kusan kashi 90% na biyan bukatun cikin gidan kasar ta Sin. Abin da ya bayyana cewa, karancin samar da hajoji masu alaka da makamashi mai tsabta matsala ce da duniya ke fuskanta, a maimakon a ce an samar da su fiye da kima. Kasashen duniya na matukar bukatar nagartaccen karfin samar da hajojin da Sin take da shi.

Damuwa da rashin kwarin gwiwa da Amurka ke da su na tilasta mata daukar matakan shafawa kasar Sin bakin fenti kan sana’o’inta da ke da fifiko, don mai da su barazanar da za ta sanya sauran kasashe fargaba. Amma, ba za a iya mai da baki fari ba, mataki daya tilo da Amurka za ta dauka wajen rage damuwarta ita ce, ta kara karfin kirkire-kirkire da hadin kai don more ci gaba tare. Kamata ya yi Amurka ta mai da hankali kan kyautata kwarewarta, a maimakon gurbata gaskiya da shafawa wasu bakin fenti, tana cewa wai hajoji masu nasaba da makamashi mai tsabta da Sin ta samar na dogaro da rangwamen da gwamnatin Sin ke bayarwa, wanda ya illata kasuwarta. To, kara karfin takara ba shi da alaka da magana ko furucin da aka yi, ya dogara ne da nagartaccen matakin da za a dauka. (Mai zana da rubuta: MINA)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka
Ra'ayi Riga

Cikar Wa’adin AGOA Ta Nuna Ra’ayin Amurka Kan Afirka

October 7, 2025
Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang
Ra'ayi Riga

Labaran Xinjiang A Zane: Manyan Sauye-Sauye A Fannin Ba Da Ilmi A Xinjiang

September 30, 2025
Alfanun Harshen Mandarin A Kasashen Afirka
Ra'ayi Riga

Alfanun Harshen Mandarin A Kasashen Afirka

September 29, 2025
Next Post
Ko Ziyarar Antony Blinken A Kasar Sin Za Ta Banbanta Da Ta Sauran Jami’an Amurka?

Ko Ziyarar Antony Blinken A Kasar Sin Za Ta Banbanta Da Ta Sauran Jami’an Amurka?

LABARAI MASU NASABA

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

Ni Ne Ɗan Siyasa Mafi Shahara A Kudu Maso Gabas, Ba Peter Obi Ba – Orji Kalu

October 9, 2025
HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

HOTUNA: Yadda Obasanjo Ya Ƙaddamar Da Sabuwar Cibiyar Taron Ƙasa Da Ƙasa A Bauchi

October 9, 2025
Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Ƙaru Da Kashi 3.9 – Bankin Duniya

October 9, 2025
Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

Tawagar Likitocin Sin Dake Saliyo Ta Gudanar Da Tiyatar Dashen Yatsa Irinta Ta Farko

October 8, 2025
Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

Babban Yankin Sin Ya Soki Lamirin Kalaman Aware Na Jagoran Yankin Taiwan

October 8, 2025
Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

Yawan Zirga-Zirgar Jiragen Kasa Tsakanin Sin Da Turai Kan Layin Dogo Na Tsakiya Ya Zarce 3,000 A Bana

October 8, 2025
Majalisa Ta Nemi Jami’an Tsaro Su Ceto Daliban Jami’ar Gusau 30 Da Aka Sace

Kafa ‘Yansandan Jihohi Na Da Matuƙar Muhimmanci Wajen Magance Matsalar Rashin Tsaro

October 8, 2025
Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

Adadin Kudaden Da Gidajen Sinima Na Sin Suka Tara Yayin Hutun Bikin Ranar Kasa Ya Haura Yuan Biliyan 1.7

October 8, 2025
Tinubu

Tinubu Na Son A Saka Hannun Jari Da Kuɗaɗen Fansho A Ɓangaren Mai Da Iskar Gas

October 8, 2025
Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

Gwamnatin Nasarawa Za Ta Hukunta Duk Masu Amfani Da Sinadiran Kamun Kifi Acikin Ruwa

October 8, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version