Daga CRI Hausa
Alkaluman babban bankin kasar Sin sun nuna cewa, harkokin da suka shafi biyan kudi ba tare da amfani da tsabar kudi ba, wadanda suka gudana karkashin bankunan kasar a shekarar 2020 da ma rubu’in da suka shude, ya ci gaba da samun tagomashi.
A cewar bankin, yawan kudin da aka biya bada tsabar kudi ba, wato ta hanyoyin da suka hada da takardu da katunan banki da intanet, ya haura yuan triliyan 4,013 a bara, kwatankwacin kimanin dala triliyan 613.84, adadin da ya karu da kaso 6.18, a kan na shekarar da ta gabata.
Ya ce cikin rubu’i na 4 kadai, yawan kudaden da aka biya ba da tsabar kudi ba, ya karu da kaso 10.29 zuwa yuan triliyan 1,069.33 akan na shekarar 2019.
Bankin ya ce biyan kudi ta wayar salula ya samu ci gaba sosai a 2020, inda jimilar kudin da aka biya ta wannan hanya, ta karu da kaso 24.5 zuwa yuan triliyan 432.16, a kan na shekarar 2019. (Fa’iza Mustapha)