Yawan Mutane Shi Ne Kasuwa
  • English
  • Business News
Wednesday, October 8, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Yawan Mutane Shi Ne Kasuwa

byCMG Hausa
2 years ago

Yayin da karin kasashen Afirka ke zurfafa cudanyar cinikayya da kasar Sin, masharhanta na kara bayyana kwarin gwiwa game da fatan shigar karin hajojin nahiyar Afirka cikin babbar kasuwar Sin. Musamman ma a wannan gaba da kamfanonin sassan biyu ke kara fadada alaka, da lalubo sabbin damammakin cin gajiya daga arzikin babbar kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya.

Yanzu haka, katafariyar kasuwar Gaoqiao dake birnin Changsha, ta zamo babban sansanin baje hajojin albarkatun gona daga kasashen Afirka, tare da bazuwarsu zuwa dukkanin sassan kasar Sin. Ana iya cewa, hakan sakamako ne na managarcin tsarin cudanyar cinikayya tsakanin Sin da kasashen na Afirka, karkashin shawarar nan ta ziri daya da hanya daya, da kuma manufofin bude kofa da Sin ke yi ga sauran sassan kasa da kasa. Baya ga tanade-tanaden dake kunshe cikin manufofin hadin gwiwar Sin da Afirka na dandalin FOCAC.

  • An Yaba Da Hadin Kan Dakarun Wanzar Da Zaman Lafiya Na Kasar Sin A Ayyukan Jin Kai Na MDD

Daya daga cikin fannoni mafiya muhimmanci da kasashen Afirka ke cin kasuwar kasar Sin a baya bayan nan shi ne cinikayyar albarkatun gona, inda ko da a baya bayan nan ma manoman kasar Kenya, suka samu zarafi na shigar da nauoin furannin daban daban cikin wannan babbar kasuwa ta kasar Sin.

Wannan kari ne kan wasu nauin mai da ake tatsa daga wasu tsirrai, wanda shi ma ake kawowa daga Madagascar, da gahawar kasar Habasha, wadanda dukkanin su ke samun karin kasuwa a Sin.

A halin da ake ciki, akwai karin kamfanonin Afirka dake kafa rassan su, tare da gudanar da hada-hadar cinikayya a kasuwar Gaoqiao dake birnin Changsha.

Ga karin manoman kasashen Afirka dake fatan shigar da albarkatun gona cikin kasuwannin kasar Sin, muna iya cewa dama ta samu, domin kuwa kasuwar kasar wadda ke kara fadada a halin yanzu tana da tagomashi, da yanayi mai kyau na bunkasa, wanda hakan zai baiwa manoman kasashen Afirka karin damammaki na samun alherai, bayan shafe tsawon lokaci suna dogaro kadai ga kasuwannin Turai da Amurka.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare
Daga Birnin Sin

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci
Daga Birnin Sin

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Next Post
Wata Sabuwar Cuta Ta Kashe Yara 10 ‘Yan Kasa Da Shekara 13 A Kaduna 

Wata Sabuwar Cuta Ta Kashe Yara 10 'Yan Kasa Da Shekara 13 A Kaduna 

LABARAI MASU NASABA

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

Sin Ta Yi Kira Ga Mambobin WTO Da Su Tinkari Yanayin Tangal-Tangal Tare

October 8, 2025
ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

ABU Na Kashe Sama Da Naira Biliyan 4 Duk Shekara A Wutar Lantarki

October 8, 2025
Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

Gwamnati Ta Roƙi ASUU Ta Soke Shiga Tsunduma Yajin Aiki, Ta Yi Alƙawarin Biyan Buƙatunsu

October 8, 2025
Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

Boko Haram Ta Taɓa Ayyana Buhari A Matsayin Wanda Zai Yi Mata Sulhu Da Gwamnati – Dalung

October 8, 2025
A Kama Wani Likitan Bogi A Neja

‘Yansanda Sun Kama Masu Laifi 153, Sun Ƙwato Miyagun Ƙwayoyi A Jihar Jigawa

October 8, 2025
An Fara Biyan Ma’aikata Sabon Mafi Ƙarancin Albashin N70,000 A Borno

‘Yansanda Da Mutanen Gari Sun Daƙile Harin Boko Haram A Borno

October 8, 2025
…ACF Ta Nesanta Kanta Da Goyon Bayan Akpabio

‘Yan Nijeriya Sama Da Miliyan 33 Ne Ke Fama Da Matsananciyar Yunwa – Akpabio

October 8, 2025
Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

Kasar Sin Ta Yi Kira Ga Kasashen Duniya Su Hada Hannu Wajen Raya Harkokin Mata

October 7, 2025
Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

Wakilin Sin Ya Ba Da Shawarwari Uku Kan Yaki Da Ta’addanci

October 7, 2025
Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

Cika Shekaru 25 Da Kafuwa: ACF Ta Jadadda Kudirinta Na Samun Hadin Kai Da Zaman Lafiya

October 7, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Exit mobile version