Yawan Shan Ibuprofen Na Iya Janyowa Maza Rashin Haihuwa –Bincike

Matasa wadanda ke yawan shan Ibuprofen, wanda magani ne da ake sha saboda a rage jin zafin ciwo, ba kuma kan ka’ida ake shan shi ba, bincike ya nunasuna iya samun matsala dangane da Haihuwa.

Sakamakon binciken an wallafa shi a Mujallar National Academy of Sciences na Amurka ya gano cewar, yawan shan Ibuprupen yana iya kawo hypogonadism, wanda wani yanayi ne da ke zama sanadiyar rashin samun haihuwa, ga kuma matsalar au’aular namiji ba zata yi aiki sosai ba, hadi da damuwa da dai sauran wasu matsaloli.

Shiga irin wannan yanayi an fi lakantashi da mashaya sigari da kuma tsofaffi, amma kuma shi wannan sabon binciken da aka yi ya nuna, abin yana iya kawo wa matasa babbar matsala.

Maganar al’amarin daya shafi maganar haihuwa an lura da shi ne daga cikin maza masu shekaru 31 da kuma wadanda basu kai 35 ba, wadanda suka sha maganin gwargwadon yadda aka kaiyade kullun na Ibuprofen  –  1200mg ko kuma kwaya shida mai 200mg ko wace kwaya zuwa makonni shida.

Daga cikin mako biyu sais u mazan nan suka kasance da hypogonadism wanda wani sinadarine na saduwa, ya samu matsala, wannan ya nuna ke nan jikinsu yana samar da testosterone da bai dace ba wani sinadari ne mai taimakawa lokacin saduwa. Maganar yawan mizanin hormone ya danganta ne da yadda shi Ibuprofen yake a jikin su, idan ya yi yawa, ba damar a samu testosterone da yawa.

Exit mobile version