CRI Hausa" />

Yawan Wadanda Aka Tabbatar Sun Kamu Da Cutar Numfashi Sun Kai Mutum 440

Ya zuwa daren ranar Talata, an tabbatar da kamuwar mutane 440 da cutar numfashin nan, wadda kwayoyin cutar “novel coronavirus” ke haddasawa, a wasu yankuna 13 dake lardin Hubei na kasar Sin.

Tuni dai cutar ta hallaka mutane 9, dukkaninsu a lardin na Hubei, kamar dai yadda mataimakin daraktan hukumar lafiya ta kasar Sin Li Bin ya bayyana, yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Larabar nan.

Ya ce bisa jimilla, a jiya Talata, an samu karuwar sabbin mutane 149 da suka harbu da wannan cuta. Kaza lika an tabbatar da kamuwar mutum guda a kasar Japan, da mutane 3 a Thailand, da kuma wani dan kasar Korea ta kudu daya.

Jami’in ya kara da cewa, an samu damar gano karuwar masu dauke da cutar ne a baya bayan nan, sakamakon ingantattun dabarun gano ta, da sanadaran tabbatar da kamuwa da ita da ake da su.

Sannan, a yayin taron, gwamnatin Sin ta gabatar da wani shirin wucin gadi na biyan kudaden jinya ga mutanen da suka kamu da cutuka masu nasaba da sabuwar annobar cutar huhu da ta bulla don ba su kulawa a kan lokaci.

A cewar hukumar kula da lafiya ta kasa, dukkan kudaden magunguna da ayyukan jinya da aka kashe wajen magance cutar ta huhu, shirin inshorar lafiya ne zai dauki nauyin biyan dukkan kudaden. (Saminu Hassan)

Exit mobile version