Rabiu Ali Indabawa" />

Yawan ‘Yan Afirka Da Ke Zuwa Amurka Ta Barauniyar Hanya Ya Karu

Adadin bakin haure ‘yan kasashen Afrika da hukumar kula da shige ta Amurka ta kama sun karu. A shekarar da ta gabata an kama mutane kasa da dari, amma a ‘yan makonnin da suka gabata, yawan mutane da aka kama sun haye mutane 600.

Tawagar ta bakin haure ‘yan Afrika wani bangare ne na mutanen da ake kamawa wadanda ba ‘yan kasashen Medico da Amurka ta tsakiya ba ne dake tsallakowa zuwa cikin Amurka ta barauniyar hanya batare da izini ba.

Duk da cewa mafi yawan bakin hauren da ake kamawa suna shigowa ne daga kasashen El Salbador da Guatemala da Honduras, yawan sauran wadanda kuma suke fitowa daga wasu kasashe na daban, ya haye kashi 4 cikin 100 na jimillar mutane kimanin 303,961 da aka kama a shekarar 2017.

A wannan shekarar da muke ciki ta 2019 mutane 593,507 aka cafke, kuma mafiyawansu sun fito ne daga kasashen Angola da Kamaru da jamhuriyar Kongo da Nijar da Najeriya da kuma Somaliya.

Exit mobile version