Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin ‘yan gudun hijirar dake tserewa hare-haren ‘yan tawaye a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, ya ninka daga dubu 30 zuwa 60 a mako daya.
Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta ce sama da mutane dubu 50 da suka tsere daga Afrika ta Tsakiyan sun tsallaka cikin Jamhuriyar Congo, daga cikinsu kuma 10 sun isa kasar ne a ranar Laraba kadai, bayan da ‘yan tawayen suka sake yunkurin afkawa birnin Bangui.
Yayin ganawa da manema labarai a birnin Geneba, Kakakin hukumar ta UNHCR Boris Cheshirkob, ya ce baya ga dubban ‘yan gudun hijirar dake Jamhuriyar Congo, akwai wasu ‘yan Afrika ta Tsakiyan akalla dubu 58 dake gudun hijira a sansanonin cikin gida, yayin da wasu dubu 9 suka tsere zuwa Kamaru.
Akalla dala miliyan 151 majalisar Dinkin Duniya ke nema don tallafawa wadanda suka tagayyara a dalilin hare-haren ‘yan tawaye a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.