Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home MAKALAR YAU

Yawon Barace-Baracen Ƙananan Yara Da Sunan Addini, Ina Mafita?

by Tayo Adelaja
October 17, 2017
in MAKALAR YAU
5 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Muhammad Awwal Umar

A ɗan tsakanin nan yawaitan ƙananan yara marabata na ƙara yawa a lunguna da soƙan ƙasar nan, hakan ya biyo bayan yadda wasu Iyaye ke ɗaukar ƙananan yara suna tura su makarantar allo ba ta da wani cikakken tsari ba, hakan ya taka rawar ganin wajen taɓarɓarewar tarbiyar yara ƙananan wanda wani lokaci rayuwarsu kan faɗa hatsari na faɗawa hannun ɓata gari ko kuma tsintar kansu a miyagun ɗabi’u.

samndaads

Gwamnatocin baya sun taka rawar ganin sosai wajen ganin an daƙile irin munanan kalaman da ake jifar ‘yan ƙasar nan musamman mutanen Arewacin ƙasar nan da shi, ko gwamnatin da ta shuɗe ta kafa harsashen buɗe makarantun allo na kwana da za a iya killace yara ba tare da barinsu suna faɗawa watangaririya ba, wanda bayan wucewarta kuma komai yayi shiru.

Mai makon abin ya ragu, ma sai ƙara yawaita da ƙara tunzura ƙananan yara wajen faɗawa haɗari na ɗaukar ƙananan yara da shekarunsu bai wuce goma zuwa sammai ba zuwa makarantun allo da ke nisa da inda garuruwansu yake, wanda duk lokacin da shugabannin suka taso sai ana danganta lamarin da addini.

A ‘yan watannin baya an salwantar da almajiran yara ƙananan ta hanyar yanka su da wuƙa, inda ake zargin har an cire ma wasu maƙogwaro a ƙaramar hukumar Rijau ta jihar Neja, wanda ya janyo gwamnatin jiha rufe wannan makarantar allon. Haka a baya-bayan nan an samu wani malamin allo da ya ɗaure almajiransa da igiyar guga yayi mai dukan da sai aka kwantar da shi asibiti tare da ceto hannayensa biyu daga salwanta saboda barazanar dakatawar jijiyoyin jini da ɗaurin ya haddasa mai.

Bincike ya tabbatar da cewar malamin ya ɗora wani haraji ne ga almajiran na sa a kowani mako wanda ake tattarawa ana baiwa matar malamin dan sayen abincin da za ta ci da ‘yayanta. Wanda rashin samun adadin waɗannan kuɗaɗen ya janyo malamin yi mai dukar da ya kusa hallakar da rayuwarsa bayan ɗauri da uƙubar yunwa saboda horon da malamin ya yiwa almajirin, wannan ya faru a ƙaramar hukumar Chanchanga ta jihar Neja.

Bayan haka an samu rahoton wani malamin allo, Malam Umaru a nan cikin ƙaramar hukumar dai ta Chanchaga da ya ajiye almajiran da ke fama da rashin lafiya ba tare da tunanin kai su asibiti kuma babu wani kyakkyawan kula wa balle samun abinci akai-akai, wanda sai da aka shiga tsakani.

Wani rahoton kuma ya bayyana yadda wani malamin allo a jihar Katsina da ya ɗaure almajirinsa a ɗaki saboda ya kasa haddace wata sura a cikin Alƙur’ani mai tsalki ba tare da kulawa ko ba shi abinci ba, wanda Allah ya baiwa almajirin hikimar kuɓucewa daga ɗaurin ya fito neman abinci ya kuma haɗu da iftila’in gobara tsawon watanni shida ke nan da har yanzu bai iya tafiya da ƙafafuwansa wanda ƙunar da yayi ya janyo mai.

Ire-iren waɗannan azabobin da almajirai ke faɗawa yana da yawa kuma da damansu babu daɗin ji, wanda hankali da tunani mai bai ɗaukar wannan salo a matsayin cigaban addini.

Shin duk da wannan matsalar mai gwamnatoci ke yi, kuma shi ya ta ke tunanin ɓullowa lamarin. Barista Mariam Haruna Kolo, ita ce babbar darakta a hukumar kula da haƙƙin yara a jihar Neja, tace mu dai a matakin gwamnati mun ƙyamaci wannan abu domin bai yi kama da addini ba, musulunci addini na gata, addini ne na karamci sannan addini wanda ya baiwa kowa ‘yanci ta hanyar ilimi. Amma yau mafi yawan malaman allon nan a gaskiya su kansu suna buƙatar su samu wayewa da tarbiya irin ta addini, sannan Iyayen yara da cin zarafin ‘yayansu ta hanyar kai su wasu garuruwa masu nisa da sunan karatu allo da su sani Allah yana kallonsu kuma yana jiransu dan yin hisabi.

Babu mutuntawa ga yaran masu ƙarancin shekaru da Iyayensu ke raba su da gida zuwa wasu garuruwa masu nisa a bar su kara zube da sunan karantun allo, wanda da daman yaran kan samu kansu a munanan yanayi na barace-barace da faɗawa haɗurra ga lafiyarsu da rayuwarsu, ni ban ga gwaninta a ɗaukar yaron da bai mallaki hankalinsa ba, bai san yadda zai iya juya taro sisi ba, bai san yadda zai iya fararen kaya su fita a ce an bar shi kara zube yana kwana kan hanya wasu ma a cikin bola da sunan karatun allo, shi ma tsarin karatun ma an cutar da shi, babu adalci a inda ake ƙuntatawa rayuwar ƙananan yara wanda ko addinin ma bai amince da hakan ba.

Malam Muhammadu Sani, wani masanin addini ne kuma mai nazari akan tarbiyar Hausawa, yace maganar gaskiya almajiranci a wannan zamani da muke ciki bai dace ga yara masu ƙarancin shekaru, kuskure mafi girma shi ne barin ƙananan yara cikin ƙuncin rayuwa na rashin walwala da kulawa. Domin yau duk inda ka ke kallon ka akwai hanya mafi sauƙi kuma zai inganta rayuwar ƙananan yara a karatun addini, domin yau ba wani lungu ko saƙo da za ka shiga ka rasa samun malamin da zai karantar da yara addini koda kai uban jahili ne kuwa.

Yaron da ya tashi gaban mahaifansa ya kan samu horo na musamman wanda shi ke bunƙasa tarbiyarsa, yana sanin ƙimar mahaifansa, yakan samu natsuwa da tausayin mahaifansa kuma yakan rayu a cikin gatan na ‘yan uwansa, saɓanin wanda aka bar shi da tunanin kanshi sai kuma ya tarbiyantu da tsoron bulala saɓanin hushin iyaye, kuma ga rayuwar ta su kan kasance cikin haɗari a kowani lokaci amma ba sa samun kulawar da za su na’am da shi.

Kodai menene ya kamata malaman mu da shugabannin da su tabbatar sun samar da wani yanayi da zai ƙananan yaran mu daga rayuwar ƙunci na azabar yunwa da wahala da shugabannin mu na gobe ke tsintar kansu domin mu dai ƙarfin mu yana ƙarewa kuma wata rana sune shugabannin in har fa ba mu tausaya masu ba, ba mu yi jinƙai gare su to lallai kar mu yi tsammanin za su ji tausayin a lokacin da ba mu iya zartar da komai.

Wani malamin addini da aka fi sani da Malam Ƙamarai yace maganar bara ga almajirai dole ayi shi, ya cigaba da cewar babbar matsalar tana hannun gwamnati ne, ya kamata ne gwamnati ta fitar da kyakkyawan tsari ta yadda ita kan ta za ta iya shigowa dan bada tallafi, domin Najeriya ƙasar musulunci ce in ko ba haka ba ban ga dalilin da zai sa ana rantsar da su da Alƙur’ani da kuma Bible ba.

Wannan barar rashin adalci ne na shugabannin ƙasar domin ba wanda ke sha’awar zama cikin ƙasƙanci amma idan ba ka da uzuri dole ka amince da yadda yanayi yazo da shi, kai yara ƙananan karatu addini bai da aibu, babban aibun shi ne yunwa da talauci da ta addabi al’umma kuma gwamnati ta kasa yin komai akai.

Koma dai menene ya kamata a riƙa mutunta ɗan Adam, domin yafi yawan yaran da ake kaiwa karatun Alƙur’ani yau suna buƙatar kulawar Iyaye fiye da komai domin sune matakin farko a tarbiya, kafin ka kai yaro makarantar allo ya kamata ya cim ma wani munzali na rayuwa ta yadda zai iya riƙe kan shi da samarwa kan shi mafita ba tare da ya dogara ga wani ba da zai iya mai mutuwar zuciya ba.

SendShareTweetShare
Previous Post

Abinci Mai gina jiki Na Sa Tsirowar Gashi Mai Kyau

Next Post

Ilollin Amfani Da Lasifikar Kunne (Earpiece)

RelatedPosts

Sulhu Da ‘Yan Bindiga: Me Ya Sa Sheikh Gumi Na Tufka Wasu Na Warwara?

Sulhu Da ‘Yan Bindiga: Me Ya Sa Sheikh Gumi Na Tufka Wasu Na Warwara?

by Sulaiman Ibrahim
5 days ago
0

Ni da ma tun da farko ban taba tunani ko...

Rance

Kura-kuren Da Hukumomi Ke Yi Wajen Bayar Da Rance

by Muhammad
1 week ago
0

Daga Aliyu M. Kurfi (PhD), Ya kamata mu sani cewa...

Ilimi

Satar Dalibai Ko  Kassara Ilimi A Arewa?

by Muhammad
1 week ago
0

alimailafiyasunusi@gmail.com - 08036064695: A yanzu babu abinda ya fi jan...

Next Post

Ilollin Amfani Da Lasifikar Kunne (Earpiece)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version