Dr. Jamilu Yusuf Zarewa" />

Yaya Hukuncin Aske Gemu Yake A Musulunci?

Tambaya:

Assalamu alaikum. Malam mene ne hukuncin tsayar da gemu? shin wajibi ne ko mustahabbi? Sannan aske shi haramun ne ko makaruhi ne? Watau yinsa banza barinsa banza.

Amsa:

Wa’alaykumussalam, To dan’uwa Annabi (SAW) yana cewa: “Ku sabawa mushrikai, ku cika gemu, ku rage gashin baki”. Kamar yadda ya zo a hadisin Bukhari mai lamba ta: 5553 da kuma Muslim a lamba ta: 259.

Wannan yasa da yawa daga cikin malamai suka tafi akan wajabcin tsayar da gemu da kuma haramcin aske shi, har ma wasu malaman kamar Ibnu Hazm sun hakaito ijma’in malamai akan haka, kamar yadda ya zo a littafinsa na Maratibul Ijma’i shafi na: 157.

Malamai suna cewa har abin da aka rawaito daga wasu sahabbai kamar Ibnu Umar cewa suna rage gemu idan ya kai wani geji, to suna yi ne lokacin hajji saboda suna ganin hakan na daga cikin rage kazantar da Alhaji ya kan yi bayan ya gama aikin hajjinsa.

Sannan gemu na daga cikin abubuwan da ke karawa namiji kwarjini da kyau, shi ya sa za ka ga wanda yake aske shi yana kama da tsohuwar da kyanta ya disashe, kamar yadda Sa’adi ya fadi a Bahjatu kulubul Abrar shafi na: 50.

Sai dai malamai suna cewa mutum yana garin da za a iya kashe shi idan ya bar gemunsa, to zai iya askewa saboda lalura, sai dai ya wajaba kowacce lalura kar ta wuce gwargwadonta.

Don neman karin bayani duba littafin: Wujubu I’ifa’ul liha

Allah ne mafi sani.

Hukuncin Baccin Bayan Sallar Asuba!

Tambaya:

Assalamu alaikum, malam INA da wata tambaya shin menene hukuncin yin bacci bayan sallar asuba? Allah ya taimaki malam!

Amsa:

To malam babu wani hadisi mai inganci wanda ya hana bacci bayan sallar asuba, sai dai bayan sallar asuba lokaci ne mai albarka, wannan yasa Annabi (SAW) idan ya yi sallar asuba baya tashi daga wurin sallar sai rana ta fito, haka ma sahabbansa Allah ya yarda da su, kamar yadda Muslim ya rawaito a hadisi mai lamaba ta: 670.

Kuma Annabi (SAW) yana cewa: “Allah ka sanyawa al’umata albarka a cikin jijjifinta” Tirmizi a hadisi mai lamba ta: 1212, kuma ya kyautata shi.

Wannan yake nuna cewa lokaci ne mai albarka, wanda bai dace da bacci ba, wannan ya sa ko da rundunar yaki Annabi (SAW) yake so ya aika, yakan aikata ne a farkon yini saboda albarkar lokacin.

Wasu daga cikin magabata, sun karhanta yin baccin bayan sallar asuba, Urwatu dan Zubair yana cewa: “Idan aka ce min wane yana baccin safe na kan guje shi’ kamar yadda Ibnu Abi-shaiba ya ambata a Musannaf dinsa 5\222.

Ya kamata ka shagala da neman ilimi ko kosuwanci a irin wannan lokacin.

Allah ne mafi sani.

Fatawar Rabon Gado (79)

Tambaya:

Assalamu alaykum, malam mutum ne ya rasu ya bar Mata 1, da diya Mace 1, sai kanne 6. ubansu 1, sai wasu kanne  7. Uwarsu 1, ya za’a raba gadon sa?

Amsa:

Wa alaikum assalam,  za’a raba abin da ya bari gida: 8, a bawa matarsa kashi daya, ‘yarsa kashi hudu, Ragowar kashi ukun sai a bawa ‘yan’uwansa da suka hada uba daya.

Allah ne mafi sani

Mace Za Ta Iya Yin Limancin Sallah?

Tambaya:

Assalamu alaikum. Malam a kaset din malam Jafar na ji ya halatta mace tai wa mata yan’uwanta limanci toh in ramadan ya zo na kan tara mata na musu, dayake duk anguwan na dan fi su karatu, toh kusan anguwan ba malamin sunna ko daya sai ‘yan bidi’a, shi ne suke nEma na baso aya ko hadisi akan hakan malam ataimakamin don Allah ?

Amsa:

Wa’alaikumus Salam To ‘yar’uwa ina rokon Allah ya jikan malam Ja’afar, mu kuma ya kyautata namu karshen, ya halatta mace ta yiwa ‘yan’uwanta mata limanci, saboda abin da aka rawaito cewa: Nana A’sha da Ummu Salama –Allah ya kara musu yarda- sun yiwa wasu mata limanci, Nawawy yana cewa wannan hadisin Baihaky ya rawaito shi a Sunan din shi, hakan Shafi’i a Musnad dinsa da sanadi mai kyau, Almajmu’u (4/187).

Haka nan an rawaito cewa Annabi (SAW) ya sanyawa Ummu-waraka ladani, sannan ya umarce ta da ta yiwa matan gidansu limanci, kamar yadda Abu-dawud ya rawaito a hadisi mai lamba ta: 491, kuma Albani ya kyautata shi.

Bisa dalilan da suka gabata za ki iya yiwa matan unguwarku limanci,  tun da kin fi su karatu, Annabi (SAW) yana cewa: “Wanda ya fi iya karatun alkur’ani shi ne zai yi limanci” Muslim 1078.

Idan za ki yi musu limanci za ki tsaya ne a tsakiyarsu in suna da yawa, in kuma ita kadaice sai ta tsaya a damarki.

Allah ne mafi sani.

Fatawar Rabon Gado (80)

Tambaya:

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuh, malam ina da tambaya, mutum ne ya mutu ya bar matan aure biyu da yayye biyar shakeekai namiji daya, sauran hudun matane, yaya rabon gadon su zai kasance

Amsa:

Wa alaikum assalam,  Za’a raba abin da ya bari kashi:4, matansa biyu su dau kashi daya, Ragowar kashi ukun sai a bawa yayyensa tun da duk dakinsu daya, duk namiji ya dau rabbon Mata biyu.

Allah ne mafi sani

Ina So Na Auri Ma’aikacin Banki, Amma Ina Tsoron Cin Haram, Ya Zan Yi?

Tambaya:

Assalamu Alaikum, Dr. Akwai wata kanwata da wani ma’aikacin banki yake so ya aura, ta bangaren mu’amalarsa za mu ce Alhamdulillah, to shi ne take neman menene halarcin auransa a shari’a? Saboda tana tsoron kar ya rika ciyar da ita da dukiyar haramun.   

Amsa:

To dan’uwa Annabi SAW yana cewa : “Allah ya la’anci mai cin riba da mai rubutata, da wadanda suka yi shaida akan haka” Muslim ya rawaito a hadisi mai lamba ta : 1598.

Hadisin da ya gabata yana nuna haramcin aiki a bankunan da suke mu’amala da riba, saboda ma’aikacin banki zai rubuta ko kuma ya shaida, ko ya taimaka wajan tsayuwar harokokin banki, kamar mai gadi, da dan aike . .

Duba fatawaa Allajanah adda’imah 15\41, da Fataawaa Islamiyya na Ibnu-uthaimin 2\401.

Idan ya zama abin da ma’aikacin banki yake amsa haramun ne, kuma ba shi da wata sana’a sai wannan, akwai hadari a auransa, saboda zai ciyar da matarsa da haramun

Malamai suna cewa duk mutumin da yake samun kudi ta hanyoyin halal da haram, idan ya maka kyauta za ka iya amsa,  saboda Annabi s.a.w. ya yi mu’amala da yahudawa, kuma a dukiyarsu akwai halal da haram, amma in ba shi da wata sana’a sai ta hanyar haram to ba za ka iya cin dukiyarsa  ba.

Wasu malaman sun halatta aikin banki a bankuna masu kudin ruwa da niyyar kawo gyara, idan niyyar mutum ta tsarkaka.

Allah ne mafi sani.

Fatawar Rabon Gado (81)

Tambaya:

Assalamu alaikum, malam  Tambaya ce dani dan Allah,, mahaifinmu  ne yarasu ya bar mata biyu kuma da ya’ya’ guda 32, maza16 mata 16.yaya rabon gadon zai kasance?

Amsa:

Wa alaikum assalam, Za’a raba abin da ya bari gida takwas, a bawa matansa kashi daya, ragowar kashi bakwan sai a bawa ‘ya’yansa su raba, duk namiji ya dau rabon mata biyu.       

Allah ne mafi sani.

Ciwo Ya Dameni, Zan Iya Amsar Bashi Da Ruwa Don Na Yi Magani?

Tambaya:

Assalamu alaikum, mutum ne yake cikin halin rashin lafiya, kuma al’ummah da suke tare ba masu taimakawa ne ba,gashi wannan ciwon nason ya hallaka shi, shi kuma ba shi da kudi kuma ba shi da hanyar kudi, malam shin zai iya karbar kudin LOAN na gobt don surika cirewa duk wata, ko babu halin haka nagode Allah yakara karfin imani da basirah.

Amsa:

Wa’alaykumussalam, Ya halatta ya amshi rancen mai ruwa, mutukar abin da yake damunsa, ya kai wancan halin da ka ambata, saboda larura tana halatta abin da aka hana, saidai ya wajaba ya amsa gwargwadon bukata.

Allah ne mafi sani.

Zarewa

Exit mobile version