Connect with us

WASANNI

Yaya Taure Ya Koma Olympiakos

Published

on

Kungiyar kwallon kafa ta Olympiakos ta gabatar da tsohon dan wasan Manchester City, Yaya Toure ga magoya bayanta bayan ya kammala kulla kwantaragi da babbar kungiyar ta kasar Girka.
Dama dai Toure ya taba buga wasa a kungiyar ta Olympiakos a can baya kafin ya raba gari da ita a shekarar 2006, in da ya koma Monaco da Barcelona tsakanin shekarar 2007 zuwa 2010.
Magoya bayan Olympiakos sun nuna farin cikinsu da isowar Toure, dan asalin kasar Cote d’Iboire kuma mai shekaru 35 da haihuwa inda suka yi ta kunna wuta tare da kewaye shi.
A karshen kakar da ta gabata ne, dan wasan ya raba gari da Manchester City bayan ya buga ma ta wasanni 230 tare da jefa kwallaye 59 kuma ya taimakawa kungiyar ta lashe kofunan firimiya guda biyu
Sai dai a baya-bayan nan, dan wasan ya koka kan yadda kungiyar ta hana shi damar buga wasanni hakan yasa kungiyar taga yakamata tabashi dama domin yatafi inda zai dinga buga wasanni.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: