Connect with us

WASANNI

Yaya Toure Makaryaci Ne -DE BRUYNE

Published

on

Dan wasan tsakiyar kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Kebin De Bruyne ya bayyana cewa tsohon dan wasan kungiyar, Yaya Taure makaryaci ne ko kuma bai san abinda yake fadawa duniya ba.

A jiya ne dai dan wasa Yaya Taure ya bayyana cewa mai koyar da yan wasan Manchester City, Pep Guardiola baya son yan wasa bakaken fata kuma yana nuna musu banbanci a kungiyar ta Manchester City.

Wannan Magana ta Yaya Taure tajawo cece-kuce a masana da masu sharhi akan kwallon kafar nahiyar turai musamman a gasar firimiya inda wasu suke ganin kamar Yaya Taure gaskiya ya bayyana yayinda wasu kuma suke ganin son zuciyarsa kawai ya fada.

Sai dai dan wasan kungiyar kuma wanda ya taimakawa kungiyar ta lashe gasar firimiyar kakar data gabata, Kebin De Bruyne ya ce Taure makaryaci ne ko kuma bai san abinda yake fada ba saboda Guardiola baya nuna banbanci.

“Idan kana kungiya kuma baka samun buga wasa yadda yakamata dole kayi zargin wani abu dole ka dinga kawo abubuwa da dama a zuciyarka domin ka kare kanka daga rashin buga wasa” in ji De Bruyne.

Ya kara da cewa “Ban taba tunanin Guardiola yanada son zuciya ba kuma ai akwai bakaken fata da yawa a kungiyar amma basu taba furta irin wannan kalma ba sai Taure”

Yaya Taure mai shekara 35 a duniya yabar Manchester City bayan ya shafe shekaru takwas a kungiyar kuma ya lashe kofin firimiya guda uku da kungiyar ta taba lashe wa a tarihi sannan kuma ya lashe kofin FA da kofin Karabawo na kasar ta Ingila
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: